--
Likitoci sun bayyana dalilinsu na  tsunduma yajin aiki ranar Litinin 02/Agusta/2021

Likitoci sun bayyana dalilinsu na tsunduma yajin aiki ranar Litinin 02/Agusta/2021



Kungiyar likitoci a kasar nan (NARD) ta umurci mambobinta dasu tsunduma yajin aikin sai baba ta gani ranar Litinin, 2 ga watan Agusta. 


An bada wannan umurnin ne ranar Asabar a karshen wani taron majalisar zartarwa (NEC) wanda aka gudanar a Umuahia, babban birnin jihar Abia kamar yadda Channels ta ruwaito. 


Da yake yiwa yan jarida bayani a karshen taron, Shugaban kungiyar, Dr Okhuaihesuyi Uyilawa ya bayyana cewa an umurci mambobin dasu fara yajin aikin sai baba ta gani.


Yace: 

"Zamu fara yajin aikin sai baba ta gani a ranar Litinin, 2 ga watan Agustan 2021. Zaku iya tunawa munyi gargadin shiga yajin aikin ranar 31 ga watan Maris 2021 sannan muka sake nanatawa a ranar 9 ga watan Afrilu, saidai tun lokacin ba'a biyan kananan likitoci albashinsu yadda ya kamata. 


"Mun samu matsala da rashin biyan albashi akan lokaci kuma a bisa gargadin da muka bada, munce ya kamata a dawo biya ta manhajar IPPS." 


Uyilawa ya kara da cewa,


 "Kuna da labari mun rasa 19 daga cikin mambonimu a sanadiyyar Korona kuma ya kamata a biya insorar mutuwa kan aiki ga magajinsu.


 

"Wancan karen da muka ziyarci ministan ayyuka da na lafiya, ance mana mambobinmu suna cikin wadanda zasu ci gajiyar inshorar amma sai muka tarar da sunayensu baya wurin. 


Ya kara da yadda gwamnatin tarayya ta gaza cimma bukatun likitoci, wannan yana daga cikin abinda yasa suka yanke hukuncin shiga yajin aikin Har ila yau, Shugaban hukumar yana baiwa yan Nijeria hakuri akan wannan hukuncin yana mai cewa gazawar gwamnati wurin sauke hakkinta ne ya janyo haka. 


Abinda aka cimma a karshen taron Bayan dukkan nazari akan rawar da gwamnatin tarayya dana jiha suka taka akan abinda ya shafi cigaban mambobinmu da kuma gazawar gwamnati wurin biyan bukatun mu bayan kwanaki dari da sha uku, majalisar zartarwa ta yanke hukuncin shiga yajin aikin sai baba ta gani daga karfe 8 na ranar Litinin 2 ga watan Agusta. 


Source: Legit

0 Response to "Likitoci sun bayyana dalilinsu na tsunduma yajin aiki ranar Litinin 02/Agusta/2021"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?