--
Cikakken Tarihin kudaden Najeriya, tun zamanin da ake amfani da gishiri a matsayin kudi zuwa yanzu

Cikakken Tarihin kudaden Najeriya, tun zamanin da ake amfani da gishiri a matsayin kudi zuwa yanzu


Alakar kudi a matsayin kadarar musaya mai daraja ya ta'allaka da yadda al'umma ke mu'amalantarsu, a Najeriya ma, batun bai sauya zane ba. 


Zai baku sha'awa da matukar burgewa ku san yadda ake hada-hada a shekarun da suka gabata a Najeriya ba tare da kudin takarda ko tsaba ko sulalla ba, da kuma yadda lamarin ya sauya zuwa yanzu. 


A cikin wannan rahoton, Legit ta tattaro daga Babban Bankin Najeriya abubuwan da ake huldar cinikayya dasu kafin zuwan kudin takarda da sulalla ko tsaba da kuma yadda aka samar da kudaden da muke kashe wa yanzu. 


1. A da an yi cinikayya da gishiri Za ku ji batun kamar almara, amma gaskiya ne. A cewar Babban Bankin Najeriya (CBN), kayayyaki kamarsu gishiri, kwalba ko kayan karau da sauran abubuwa sun kasance abubuwa masu daraja a madadin kudi kafin zuwan turawan mulkin mallaka. 


2. Zuwan karfe; sulalla A farkon zuwan sulalla, Bankin Ingila ke lura da su kuma ke samar dasu a matsayin wata harkalla mai zaman kanta. Wannan ya ci gaba har zuwa shekarar 1912. 


3. Zuwan kudin takarda mallakar turawa Kamar dai sauran kasashen Afrika ta Yamma, mafi girman kudin takarda da Najeriya ta fara mallaka shi ne fam. A bangare guda, sule kuwa shi ne mafi darajan tsaba na karfe. 


4. Kudin takarda mallakar Najeriya A shekarar 1959 Najeriya ta fara samar da kudin takarda mallakarta, duk da cewa, hakan bai gama kankama ba har sai shekarar 1962 lokacin ne kudin ya fara nuna Najeriya a matsayin jamhuriya mai 'yanci. Sabanin yanzu, a da ana rubuta Tarayyar Najeriya a jikin kudi. 


5. Zuwan N1, N5 da N10 Kudin takarda a Najeriya ya fara zuwa ne cikin samfuri uku, wato; N1, N5 da N10. Hakan ya bayyana ne a ranar 2 ga watan Yulin 1978. A shekarar 1977, aka kaddamar da gudan N20. 


6. Zuwan kudin leda A ranar 28 ga watan Fabrairun 2007, N20 ta leda ta fara bayyana a Najeriya, wacce har yanzu ita ake kashe wa. Hakazalika an fitar da sabbin tsarin kudaden karfe na N1 da kwabo 50. 


7. Zuwan N50 ta leda 


Yayin da Najeriya ta cika shekaru 50 da samun 'yancin kai, a lokacin ne aka fitar da sabuwar samfurin N50 ita ma ta leda kamar dai N20, a ranar 29 ga watan Satumban 2010. Daga baya kuwa aka sauya tsarin N100 ta Najeriya zuwa wani sabon tsari. 

0 Response to "Cikakken Tarihin kudaden Najeriya, tun zamanin da ake amfani da gishiri a matsayin kudi zuwa yanzu "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?