--
Duba yadda Hukumar hisbah ta damke wani mai kyamis da ke lalata da mata a Kano

Duba yadda Hukumar hisbah ta damke wani mai kyamis da ke lalata da mata a Kano


Hukumar Hisbah a Jihar Kano ta tabbatar da kama wani mai sana’ar shagon sayar da magunguna mai suna Yahata Zakari 


An kama Zakari ne bisa zargin amfani da wani gida sabanin kyamis din wajen lalata da mata An yi kamen ne bayan mazauna yankin sun kai kararsa kan zargin 


Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta cafke wani Yahaya Zakari bisa zargin kai wata mata gidansa da ke Sabuwar Gandu a birnin Kano, jaridar Punch ta ruwaito. 


Babban kwamandan hukumar, Dakta Haruna Ibn-Sina, ya tabbatar da kamun a cikin wata sanarwa da ya fitar a Kano ranar Juma’a. 


Jaridar Aminiya ta kuma ruwaito cewa mazauna unguwar dai sun yi zargin cewa mutumin ya jima yana aikata ta’asar inda ya ware gidan wanda babu kowa a ciki yana kai mata da nufin zai duba su a ciki. 


An mika kwafin sanarwar, wacce Malam Lawal Ibrahim, jami’in hulda da jama’a na hukumar ya sa wa hannu, ga Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya. 


A cewarsa, an yi kamen ne bayan rahotanni daga mazauna yankin. "Matar ta je siyan magunguna daga kyamis din Zakari lokacin da ya kai ta gidansa," in ji shi. 


Ibn-Sina ya nuna rashin jin dadinsa kan lamarin da ake zargin mutumin da shi, inda ya tabbatar da cewa hukumar za ta gudanar da cikakken bincike kan lamarin. 


Don haka ya shawarci iyaye da su sanya ido sosai kan zirga -zirgar ‘ya’yansu, musamman yara mata, don hana aukuwar abubuwan da ba a so. 


Source: Legit

0 Response to "Duba yadda Hukumar hisbah ta damke wani mai kyamis da ke lalata da mata a Kano "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?