--
Ta sa hakori ta gutsirewa mijinta mazakuta saboda ya gaza kashe bera a dakinta

Ta sa hakori ta gutsirewa mijinta mazakuta saboda ya gaza kashe bera a dakinta

Rikici ya kaure tsakanin Abraham Musonda (52) da matarsa mai shekaru 40, sakamakon gaza cire mata bera da ta gani a kusa da gadonta

A tsakiyar rikicin ne, matar mai suna Mukupa ta fusata, ta sa hakori ta gutsirewa mijin na ta mazakuta, saboda gaza cire mata beran

A cewar jaridar Metro UK, an garzaya da Mr Musonda asibitin Kitwe, domin ba shi agajin gaggawa Rikici ya kaure tsakanin Abraham Musonda (52) da matarsa mai shekaru 40, sakamakon gaza cire mata bera da ta gani a kusa da gadonta, a gidansu da ke garin Kitwe, kasar Zimbabwe.

A tsakiyar rikicin ne, matar mai suna Mukupa ta fusata, ta sa hakori ta gutsirewa mijin na ta mazakuta, saboda gaza cire mata beran, a cewar rundunar 'yan sanda.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa matar ta yi ikirarin beran yana takura mata tare da hanata rawan gaban hantsi, musamman lokacin da ta dawo daki ta same shi a gefen gadonta.

Duk wani kokarinta na yin bacci a wannan dare ya gagara, sakamakon guje gujen da beran ke yi a cikin dakin, lamarin da ya tilasta ta kiran mijin nata, don ya fitar da shi, a cewar ta.

Amma da mijin ya ki amincewa da wannan bukata, sai Mukupa ta samu damar kafa hakoranta a mazakutarsa, lamarin da ya jawo ya samu rauni mai muni.

Bothwell Namuswa, mataimakin kwamishinan 'yan sanda na shiyyar Copperbelt, ya shaidawa manema labarai cewa ma'auratan sun rabu,

amma suna zama a gida daya, daki daban daban. A cewar jaridar Metro UK, an garzaya da Mr Musonda asibitin Kitwe, domin ba shi agajin gaggawa kan wannan mummunan al'amari.

A wani labarin makamancin wannan, 'yan sanda a kasar sun cafke wani mutum da ya duki yaron budurwarsa, har ya tsinke masa mazakuta da kunbarsa. .

Mohammad Mahmoud Shaar, na yankin Coconut Creek, Florida, ya ajiye budurwasa a wajen aikinta a ranar Alhamis, kana ya dauki yaronta mai shekaru hudu ya kaishi gidan raino.

Shaar sai ya farmaki yaron a lokacin da ran sa ya baci bayan da mahaifiyar yaron ta sauka daga motar, a cewar rahoton cafke mutumin. Ofishin 'yan sandan Sheriff na yankin Broward ya ce gidan rainon na da tazarar mil 1.6 daga wajen aikin mahaifiyar, amma sai da Shaar ya kwashe mintuna 20 kafin ya isa.

Mai rainon yaron ta ce taga yaron yana kuka cikin firgici, kuma Shaar ya ajiye shi ba tare da ya yi mata bayanin abunda ya faru ba, ya yi tafiyarsa.

Source: Legit.ng

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Ta sa hakori ta gutsirewa mijinta mazakuta saboda ya gaza kashe bera a dakinta "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?