--
Cigaba: Ganduje ya saka na'urorin sa-ido a manyan titunan Kano, bidiyon yadda suke aiki

Cigaba: Ganduje ya saka na'urorin sa-ido a manyan titunan Kano, bidiyon yadda suke aiki

Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya kammala saka na'urorin sa-ido a kan wasu daga cikin manyan titunan birnin Kano domin inganta tsaro da saukakawa jami'an tsaro aiki.

A wani takaitaccen sako da Salihu Tanko Yakasai, hadimin Ganduje, ya wallafa a shafinsa na tuwita, an nuna bidiyon yadda jami'an 'yan sanda ke kallon motsin mutane da ababen hawa a manyan titunan jihar,

"Duk da Kano tana cikin jihohin da ke da zaman lafiya a Najeriya a shekaru 5 da suka gabata, mai girma gwamna Abdullahi Umar Ganduje bai daina kokarin kara karfafa tsaro a jihar Kano ba, saboda gwamnatinsa ta saka na'urorin sa-ido a manyan titunan birnin Kano.

"Ana sarrafa na'urorin daga dakin na musamman a hedikwatar 'yan sandan Kano," kamar yadda Yakasai ya bayyana.




 Ko a kwanakin baya gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da cewa ta saka irin wadannan na'urori a cikin birnin Kaduna domin inganta tsamo.



Jalama'a da dama da suka yi magana a kan sakon da Yakasai ya wallafa, sun yabawa kokarin gwamna Ganduje na zamanantar da tsaro a Kano.


Wasu daga cikinsu sun yi kira da sauran gwamnonin jihohin arewa su yi koyi da irin wannan cigaba da Ganduje ya kawowa Kano, a cewarsu, hakan zai taimaka wajen saurin gano batagari da kuma daukan mataki a kan lokaci

A daren ranar Lahadi ne hedikwatar rundunar tsaro ta kasa (DHQ) ta sanar da cewa ta tsaurara matakan tsaro a Abuja da wasu makwabtan jihohi bayan samun labarin cewa kungiyar Boko Haram tana shirin kai wasu hare-hare.

DHQ ta ce ta gaggauta daukan wannan mataki ne bayan hukumar kwastam ta Najeriya (NCS) ta fitar da wata sanarwa domin ankarar da mazauna Abuja da wasu makwabtan jihohi a kan shirin kai hare-haren.

Manjo Janar John Enenche, kakakin DHQ, ya ce rundunar soji ta sanar da dukkan dakarunta su kasance cikin shirin 'ko ta kwana'.

A cikin wata sanarwa da hukumar Kwastam ta fitar, ta ce mayakan kungiyar Boko Haram suna shirin kaddamar da wasu hare-hare a Abuja, jihar Kogi da kuma jihar Nasarawa.

Sai dai, a cikin jawabin da Enenche ya fitar ranar Lahadi, DHQ ta bayyana cewa za ta yi kokarin dakile kai hare-haren.


Source: Legit.ng

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Cigaba: Ganduje ya saka na'urorin sa-ido a manyan titunan Kano, bidiyon yadda suke aiki "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?