LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Rashin lafiya: An fitar da ministan ilimi, Adamu Adamu, kasar waje

A
An fitar da ministan ilimi, Adamu Adamu, zuwa kasar Jamus domin a duba lafiyarsa, kamar yadda SaharaReporters ta rawaito

SaharaReporters ta rawaito cewa wannan shine karo na uku da aka fitar da ministan zuwa turai a 'yan watannin baya bayan nan

Adamu Adamu ya na daga cikin minsitoci da ke da kusanci da kuma kyakyawar alaka da shugaban kasa, Muhammadu Buhari Sahara Reporters ta wallafa rahoton cewa yanzu haka ministan ilimi na kasa, Adamu Adamu, ya na zaman jinya a kasar Jamus.

A cikin wani rahoto da SaharaReporters ta wallafa ranar Litinin, ta bayyana cewa an kwantar da Adamu Adamu a wani asibiti da ke birnin Berlin.

A cewar SaharaReporters, wannan shine karo na uku da aka fitar da ministan zuwa kasar Jamus domin a duba lafiyarsa tun bayan barkewar annobar korona. Wata majiya ta sanar da SaharaReporters cewa ministan yana fama da matsalar koda. Sai dai, duk da hakan, har yanzu babu tabbacin wanne ciwone ya ke yawan fitar da ministan zuwa Turai domin a duba lafiyarsa.

Harkoki da yawa da suka shafi bangaren ilimi sun tsaya cak saboda ministan baya nan. Jaridar SaharaReporters ta wallafa cewa shirye-shiryen komawa makaranta sun tsaya a yayin da ake tsammanin dawowar ministan nan bada dadewa ba.

"Wannan shine karo na uku da aka fitar da ministan zuwa kasar Jamus tun bayan barkewar annobar korona. "A daya daga cikin irin tafiye-tafiyen da ya yi, ya yi amfani da wani karamin jirgi mallakar wani tsohon shugaban wata jami'ar Najeriya.

"Yanzu hakan ya na kwance zaman jinya a wani asibiti da ke birnin Berlin a kasar Jamus, amma ana boye maganar, musamman dalilin yawan fitarsa zuwa Turai a kwanakin baya bayan nan.

"Abubuwa da dama da suka shafi bangaren ilimi, musamman shirin bude makarantu, sun tsaya saboda ministan ilimi ba ya nan," a cewar majiyar gwamnati, kamar yadda SaharaReporters ta wallafa.

Adamu Adamu ya na daga cikin ministoci ma su kusanci da shugaban kasa, Muhammadu Buhari. An yi tsammanin cewa Buhari zai nada Adamu Adamu a matsayin sabon shugaban ma'aikatan fadarsa bayan mutuwar marigayi Abba Kyari.

Source: Legit.ng

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments