LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Saurayi ya sassara budurwarsa a kan zarginta da asirin tsotse masa mazakuta


Wata mahaifiyar yara biyu da ke cikin shekarunta na 30 na kokarin ganin yadda za ta tashi muguwar jinyar da ta fada bayan rikicin da tayi da saurayinta kuma uban 'ya'yanta. Saurayin nata ya sassarata da gatari bayan da suka samu matsala a kan zarginta da yayi da amfani da asiri wurin tsotse masa mazakuta.


Budurwar da ke fama da jinya mai suna Augsutina Jowho Broma, tana fama da sarar da saurayin nata yayi mata a kai da kashin baya. Anthony Edijala mai shekaru 39 ya shiga hannun 'yan sanda bayan muguwar aika-aikar da yayi wa budurwarsa,

kuma mahaifiyar 'ya'yansa biyu. Wani dan uwan budurwar mai suna Felix Broma, ya bayyana cewa an kwashi 'yar uwarsa rai a hannun Allah zuwa babban asibitin Ughelli, inda take samun taimakon likitoci.


Ya tabbatar da cewa, yana tsoron shanyewar bangaren jiki ga 'yar uwarsa sakamakon jerin ayyukan da aka mata. Ganau ba jiyau da suka ga yadda lamarin ya auku, sun sanar da Vanguard cewa sai da 'yan sanda suka zo wurin sannan suka samu damar karbar saurayin daga hannun jama'ar da suka nada masa mugun duka.
A yayin tabbatar da aukuwar lamarin ga jaridar Vanguard, majiya daga jami'an tsaro ta ce wanda ake zargin ya amsa laifinsa, kuma ya ce sun yi fada da budurwar tasa wanda hakan yasa kowa ya kama hanyarsa. Amma kuma daga bisani, ya gane cewa laifinsa ne a dukkan fadan da suka yi.

Majiyar da ta bukaci a boye sunanta, ta ce, "Yana zargin budurwarsa da yin asirin da ya tsotse mazakutarsa wacce yace a baya ta fi hakan girma. Hakan ne yasa suka yi baran-baran.
"A ranar da lamarin ya faru, ya je shagon da take saide-saide domin ganin 'ya'yan da suka haifa. Atake rikici ya barke inda budurwar ta fito da gatari domin kare kanta. "Babu kakkautawa wanda ake zargin ya karba gatarin tare da sassara mata a kai da kashin baya."Source: Legit.ng

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments