LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Mutum biyu sun riga mu gidan gaskiya sakamakon harin da ƴan IPOB suka kai wa hausawa a Rivers

A ƙalla hausawa biyu mazauna Oyigbo a ƙaramar hukumar Oyigbo ta jihar Rivers ne suka riga mu gidan gaskiya sakamakon harin da wasu da ake zargin ƴan kungiyar masu fafutikan kafa ƙasar Biafra, IPOB, suka kai musu a Oyigbo.


Wani ganau ya bayyana cewa fusatattun mambobin na ƙungiyar IPOB sun kai wa Hausawa mazauna Oyigbo hari a ranakun Asabar da Lahadi.

Ganau ɗin ya ce an kashe aƙalla mutane biyu yayin da wasu da dama sun samu munannan raunuka kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

"Ranar Asabar aka fara kai harin sannan aka cigaba zuwa Lahadi. Wasu matasa da ake zargin ƴan IPOB ne sun kai hari wata unguwa da Hausawa suka fi yawa dauƙe da miyagun makamai. Mutum biyu sun mutu yayin da wasu sun jikkata," in ji shi.

Mai magana da yawun hausawa a jihar Rivers, Alhaji Musa Saidu ya yi Allah wadai da harin yayin da ya ke tabbatar wa majiyar Legit.ng Hausa afkuwar lamarin.

Alhaji Musa Saidu ya ce wasu matasa da ake zargin ƴan IPOB ne suka kashe mutanen biyu sakamakon harin da suka kai musu a Oyigbo.

Ya ce bai san dalilin da yasa suka kai musu harin ba amma yana tunanin ba zai rasa nasaba da barazanar da ƴan kungiyar ta IPOB suka yi wa hausawan mazauna Rivers ba a baya. Ya yi kira da rundunar ƴan sanda ta yi bincike ta gano wadanda suka kai harin ta kuma hukunta su.

Duk yunkurin da aka yi na tuntubar Kakakin rundunar ƴan sanda na jihar Rivers, SP Nnamdi Omoni a wayar tarho don jin ta bakinsa ya ci tura.

A bangarensa, shugaban ƙaramar hukumar Oyigbo, Prince Gerald Oforji ya yi tir da harin da aka kai wa hausawan inda ya bukaci su zauna lafiya kuma kada su dauki doka a hannun su.

A wani rahoton daban kun ji wasu ƴan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kai hari asibitin koyarwa ta jami'ar Ilorin a ranar Alhamis 3 ga watan Satumba sun sace Sarkin Fulanin Ilorin, Usman Adamu Harɗo.

Ƴan bindigan sun kai harin ne misalin karfe 8 na safe kamar yadda Linda Ikeji ta ruwaito. Rahotanni sun ce Sarkin Fulanin yana hanyarsa ta zuwa banki ne a cikin mota tare da ɗansa Babangida yayin da wasu ƴan bindigan suka tare motarsu.


Source: Legit.ng

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments