--
Karfin hali: Wani mutumi ya bindige matarshi har lahira a cikin ofishin 'yan sanda yayin da taje kai karar shi

Karfin hali: Wani mutumi ya bindige matarshi har lahira a cikin ofishin 'yan sanda yayin da taje kai karar shi


Mijin da matarshi ta je ofishin 'yan sanda domin kai karar shi akan abubuwan da yake yi mata 


Ya bita har cikin ofishin 'yan sandan ya harbeta da bindiga a gaban jami'an 'yan sanda 


Sai dai kuma an samu nasarar kama shi kuma an samu nasarar kwace bindigar daga hannun shi Wani irin lamari mai cike da tashin hankali ya faru a ofishin 'yan sanda na Madeira dake Mthatha,


cikin kasarAfrika ta Kudu, yayin da wani mutumi ya harbe matar shi mai shekaru 28, a cikin ofishin 'yan sandan a lokacin da taje kai karar shi.


Mutumin wanda aka bayyana cewa yana aikin gadi ne a wani kamfani, an kama shi a cikin ofishin 'yan sandan, bayan ya karar da harsashin cikin bindigar akan matar. 


Wasu shaidu da lamarin ya faru a gabansu lokacin da suke ofishin 'yan sandan, sun ranta ana kare a kokarin da suke na tsira da rayukansu.


Wani da lamarin ya faru a gabanshi mai suna, Songezo Sanazo ya bayyanawa jaridar Dispatch Live cewa:


"Ina wajen ina kokarin karbar wasu takardu kawai sai naji harbin bindiga. "Na jiyo na farko, na dauka ba komai bane. 


Amma sai na gudu na boye a jikin bango a lokacin dana jiyo tashin bindigar a karo na biyu, na uku dana hudu ya sanya mutane suka fara gudun tsira da rayukansu suna ihun neman taimako. Dukkan mu hankulan mu sun tashi matuka." 


Kakakin rundunar 'yan sandan, Birigediya Tembinkosi Kinana wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce mutumin ya yi kokarin guduwa kafin a samu nasarar cafke shi, bayan yayi harbin a ranar Litinin 7 ga watan Satumba. 


Ya ce: "A lokacin da ta shigo take sanar da jami'in dan sanda halin da take ciki. mijin ya shigo ofishin ba tare da yace komai ba ya fara harbin matar, wacce ta ji ciwuka da dama a wajen. 


"An samu nasarar kwace bindigar da ya shiga wajen da ita, inda kuma za a gabatar da bincike a kan shi." 


Kinana ya ce mai laifin zai bayyana a gaban kotu bisa zargin shi da ake yi da aikata kisan kai da zarar sun kammala bincike akan wannan lamari mai ban tsoro da. 


Source: Legit.ng

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Karfin hali: Wani mutumi ya bindige matarshi har lahira a cikin ofishin 'yan sanda yayin da taje kai karar shi "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?