--
 Abin ya isa, ya kamata a fatattaki Hafsun Sojojin da su ka gaza inji Kungiyar CNCE

Abin ya isa, ya kamata a fatattaki Hafsun Sojojin da su ka gaza inji Kungiyar CNCE


Ganin yadda ake fama da matsalar rashin tsaro har gobe, wata kungiya mai suna CNCE ta manyan Arewa, ta yi kira ga shugaban kasa ya sauya hafsun sojoji.


Kungiyar CNCE ta dattawan Arewa maso tsakiyar Najeriya ta na ganin sauke shugabannin sojoji shi ne zai taimaka wajen ganin an samu tsaro da cikakken zaman lafiya. 


Jaridar Vanguard ta ce wannan bayani ya fito ne a wani jawabi daga bakin shugaban kungiyar CNCE, Usman Bida da sakatarensa, Moses Okudu, jiya a garin Abuja. 


Kungiyar ta fito ta yi wannan magana ne bayan da jami’an kwastam su ka sanar da hukumomi cewa ana zargin ‘yan ta’addan Boko Haram sun shigo yankin Abuja. 


“Mu na tare da sauran ‘Yan Najeriya, mu na kiran shugaban kasa ya yi maza ya canzawa hukumomin tsaro zani ta hanyar tsige hafsun sojoji a matsayin matakin farko.” Kungiyar CNCE ta ce: 


“’Yan Najeriya sun gaji da gafara sa, ba su ka ga kaho ba a sha’anin tsaro.” “Mu na takaicin yadda babu wata jiha a tsakiyar Arewa da ba a samun harin ‘yan ta’adda ko kuma a kashe Bayin Allah haka kawai, yankin da a baya ya fi kowane zaman lafiya a Arewa.” 


CNCE ta ce jim kadan da samun labarin kama ‘yan ta’adda fiye da 400 da mugayen makamai a Nasarawa, sai kuma ga jita-jitar Boko Haram sun shiga Abuja da kewaye. 


Wannan kungiya ta cigaba da jawabi cewa: "A yau hankalin mutanen Najeriya da wadanda si ke zaune a Arewa maso tsakiya ya tashi da wannan labari” “Ba a shiga wasu bangarorin Nasarawa, Neja, Kogi saboda ‘yan ta’adda su na kisa, sata, da garkuwa da mutane,


sai ka ce mu na zaman dawa.” Inji CNCE. “Mun zabi shugaba Muhammed Buhari ne saboda kwarewarsa a sha’anin tsaro da gaskiyarsa, kuma mu na sa ran mu ga ya yi kokari.”


Kungiyar ta ce mu na tare da shi har gobe. “Mu na kira ga shugaban kasa, babu yadda za a ce jami’ai hudu sun fi duka dubunnan sojojin da mu ke da su kwarewa, a kan wannan gaba ne mu ke kira ka sauke hafsun da ba su san aiki ba.” 


Source: Legit.ng

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to " Abin ya isa, ya kamata a fatattaki Hafsun Sojojin da su ka gaza inji Kungiyar CNCE "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?