LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Yanzu-yanzu: An garzaya da Aisha Buhari Dubai jinyan rashin lafiya

An garzaya da uwargidan shugaba Muhammadu Buhari, Hajiya Aisha Buhari, birnin Dubai, kasar UAE don jinyan ciwon wuyan da take fama da shi tun bayan zuwanta Legas, Daily Trust ta ruwaito.

An samu labarin cewa uwargidan shugaba Muhammadu Buhari ta tafi Dubai ne tun washe garin Sallah sakamakon ciwon wuya da take fama dashi bayan komawa birnin tarayya Abuja daga jihar Legas.

Za ku tuna cewa a watan Yuli, Aisha Buhari ta kai ziyarar ta'aziyya ga Mrs Florence Ajimobi, uwargidan tsohon gwamnan Oyo, Abiloa Ajimobi, a gidansu dake Glover ROad, Ikoyi, jihar Legas. Ajimobi ya rasu ne ranar 25 ga Yuni sakamakon jinyan da yayi bayan kamuwa da cutar Coronavirus.

Yayinda ta koma Abuja, ta killace kanta na tsawon makonni biyu saboda ciwon wuyan da take fama da shi na kimanin wata daya bayan ta'aziyyar.

 Abin ya tayar da hankalin na kusa da uwargidar kuma hakan ya sa aka garzaya da ita birnin Dubai don ganin Likita.

SOURCE: LEGIT.NG 

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN


KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments