LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Gagara: Yanda Fusataccen mahaifi ya datse hannun dansa

Wani mutum mai suna Sunday Brown mazaunin yankin Nyomidibi a unguwar Nyangasang da ke garin Calaba, babban birnin jihar Kuros Riba, ya datse hannun dansa mai suna Mathew saboda ya shiga kungiyar tsafi.

Lamarin ya faru ne da safiyar ranar Alhamis bayan Mista Brown da dansa, Mathew, sun yi fito-na-fito kamar yadda su ka saba. Wani makwabcin Mista Brown ya shaidawa manema labarai cewa rigimar da ke tsakanin uba da da ta fara zama barazana ga mazauna unguwar,

saboda yanzu haka abokan matashin sun fara barazanar daukan fansa. Majiyar ta bayyana cewa shigar Mathew kungiyar tsafi da sauran halayensa na gagara sune suka jawo mahaifinsa ya datse ma sa hannu.

Wani shugaba a unguwar, Timothy Sam, ya shaidawa manema labarai cewa jami'an rundunar 'yan sanda sun sha kama saboda gagararsa da kuma yawon dare mai cike da alamun tambaya.

"Da sanyin safiyar ranar Alhamis ne Mathew ya kai wa mahaifinsa harin daukan fansa.

"Shi kuma mahaifin ya datse masa hannu a kokarinsa na kare kansa," a cewarsa. Kokarin manema labarai na jin ta bakin mista Brown Mathew bai samu ba. Kakakin rundunar 'yan sanda, Irene Ugbo, ta ce ba ta samu labarin faruwar lamarin ba, amma ta dauki alkawarin gudanar da bincike.

SOURCE: LEGIT.NG 

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN


KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments