LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Yadda barawo ya kwace jakar kudi $200,000 a hannun wani mutum bayan ya fito daga Banki

Wani bawan Allah mai suna Francisco Cornejo ya rasa iya kudin ajiyarsa a rayuwarsa bayan wani barawo ya kwace jakar kudin lokacin da mutunin ya karbo kudin ya fito daga cikin Banki a Chase Bank da ke  Huntington Park a California na kasar Amurka.

Francisco ya sayar da gidansa hadi da sauran kudin ajiyarsa a tsawon rayuwarsa har Dalan Amurka  $200,000, amma bayan ya fito daga cikin Bankin rike da jakarsa da ya sa kudi, kwatsam sai wani barawo da ya rufe fuska da jikinsa ya kwace jakar ya ruga da gudu.

Faifen bidiyo na kamarar tsaro na CCTV ya dauki hoton lamarin kuma yansanda na amfani da hoton bidiyon yadda lamarin ya faru domin gudanar da bincike.

SOURCE: ISYAKU.COM

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN


KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments