LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Ka yi abinda ya kamata APC ta lashe zabe a Edo - Buhari ga Ganduje

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi kira da jam'iyyar All Progressive Congress (APC) a jihar Edo su kiyayi irin abinda ya faru a jihar Rivers, Bayelsa da Zamfara a baya.

Shugaban kasan ya bayyana hakan ne yayinda ya karbi bakunicn dan takaran kujeran gwamnan Edo karkashin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) , Fasto Osagie Ize-Iyamu.

Gwamnan jihar Yobe kuma shugaban kwamitin rikon kwaryar jam'iyyar APC, Mai Mala Buni, ne ya kawo Ize-Iyamu fadar shugaban kasa.

Daga cikin tawagar akwai shugaban kwamitin yakin neman zaben gwamna jihar Edo kuma gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje da shugaban kungiyar gwamnonin APC kuma gwamnan Kebbi, Abubuakar taiku Bagudu.

A jawabin da Buhari yayi ta hannun mai bashi shawara kan kafafen yada labarai, Femi Adesina, da Channels TV ta gani, ya yi kira da shugabannin jam'iyyar da na yakin neman zaben suyi abinda ya kamata domin tabbatar da cewa an samu nasara a zaben.

Ya yi kira da shugabannin jam'iyyar su kiyayi irin zamewan da jam'iyyar tayi a jihohin RIvers, Bayelsa da Zamfara a 2019.

Buhari ya taya Osaze Iye-Iyamu murnan nasarar da yayi a zaben fidda gwanin jam'iyyar kuma ya bashi tabbacin goyon bayansa.

Shugaban kwamitin rikon kwaryan jam'iyyar APC, Mai Mala Buni, ya bayyanawa shugaba Buhari cewa: "Fasto Ise-Iyamu kwararren dan siyasa ne wanda al'ummarsa ke son sa."

Hakazalika shugaban kwamitin yakin neman zaben jihar Edo, Gwamna Ganduje, ya ce bisa ga ka'idojin jam'iyyar, APC za ta gudanar da yakin neman zaben cikin zaman lafiya da lumana ba tare da cin mutuncin wani ba.

Ganduje ya ce tuni an kaddamar da yakin neman zabe kuma jam'iyyar ce mai rinjaye a majalisar dokokin jihar da mambobi 17 cikin 24.

SOURCE: LEGIT.NG 

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN


KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments