LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Turmi da tabarya na kama shi da diyarsa, shiyasa na rabu da shi - Matar basarake

Jami'an 'yan sanda a jihar Ogun sun damke dagacin kauye, Rasheed Sholabi, a kan zarginsa da ake da lalata diyar cikinsa mai shekaru 15.

Sholabi na da sarautar Baale of Oose Agbedu Ajibawo a yankin Owode-Yewa da ke karamar hukumar Yewa ta Kudu ta jihar, jaridar The Nation ta ruwaito.

An gano cewa 'yan sandan sun kama dagacin ne bayan rahoton da diyarsa, wacce ta shiga ofishin 'yan sanda da ke Owode Egbado ta kai. Ta sanar da cewa mahaifinta yana lalata da ita tun tana karamarta.

A wata takarda da kakakin rundunar 'yan sandan jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi, ya fitar a jiya a Abeokuta, ya ce yarinyar da bakinta ta sanar da cewa mahaifinta ya fara lalata da ita tun tana da shekaru 11. Yarinyar tace, tana da babbar matsala da mafitsararta saboda abinda mahaifinta yake mata.

"Yarinyar ta sanar da 'yan sanda cewa mahaifiyarta ta rasu tun kafin ta kai shekaru biyu kuma mahaifinta ya hana kowa daukarta,"

Oyeyemi yace. Kakakin ya ce, bayan wannan korafin, SP Olabisi Elebute, ya jagoranci jami'ansa don kama Sholabi. Ya fara musanta zargin a farko amma har suma sai da yayi yayin da diyarsa ta tsaya gabansa kuma aka tabbatar da an samu shaida daga tsohuwar matarsa.

"Tsohuwar matarsa ta sanar da 'yan sanda cewa ta kama shi turmi da tabarya yana lalata da diyarsa kuma wannan dalilin ne yasa ta tsere ta bar shi,"


Oyeyemi yace. Ya kara da cewa, an mika yarinyar gidan marayu don kula da ita. Oyeyemi ya kara da cewa, kwamishinan 'yan sandan jihar Ogun, Edward A. Ajogun, ya bukaci a mika lamarin gaban sashen bincike a kan cin zarafin kananan yara da safararsu.


SOURCE: LEGIT.NG

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN


KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments