LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Rashin tsugunawa don bada zobe: Budurwa ta ki amincewa da bukatar aure

Abubuwan mamaki basu taba karewa a duniya, kuma idan da ran ka za ka sha kallo

Wani bidiyo da ke yawo a kafafaen sada zumuntar zamani ya janyo cece-kuce a tsakanin samari da 'yan mata

A bidiyon, budurwar ta ki karbar zoben saurayin don amincewa da bukatar aurenta da yake saboda bai durkusa mata ba

Wani bidiyo a cikin kwanakin nan da ke yawo a kafafen sada zumuntar zamani ya bai wa jama'a mamaki.

A bidiyon, an ga mutumin yana mika bukatar auren budurwarsa a kasan bishiya, amma sai ya sha mamakin da bai taba tsammani ba.

Kamar yadda bidiyon ya nuna, mutumin na mika bukatar ne ta hanyar mika mata zobe yayin da dukkansu ke tsaye amma sai budurwar ta ki karba.


Ta bukaci saurayin da ya durkusa a kan guiwoyinsa yayin mika mata zoben.

Wani mutum wanda ake tsammanin shi ya nadi bidiyon da wayarsa, ya shawarci saurayin da ya gurfana a kan guiwoyinsa kamar yadda budurwar ta bukata, amma yace Allah ya kashe shi a take ba zai durkusa ba.

SOURCE: LEGIT.NG 

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN


KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments