LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Dan wasan Chelsea, Willian ya amince zai koma Arsenal a kwantirakin shekaru uku

Kungiyar Arsenal ta gama yarjejeniyar siyan tauraron Chelsea wato Willian a karshen wannan kakar. Dan wasan mai shekaru 31 ya amince zai koma tawagar Mikel da kwantirakin shekaru uku yayin da zasu ringa biyan shi euros miliyan 100,000 a kowane mako.

Arsenal sun kagara dasu kammala maganar siyan dan wasan, kuma Lampard bai ba shuwagabannin shi goyon baya ba wurin biyan bukatun Willian, yayin da Willian ya bukaci kwantirakin shekaru uku amma Chelsea shekaru biyu kadai suke shirin kara mai.

Hakan ne yaba Mikel Arteta damar jawo ra’ayin dan wasan domin ya fahimci cewa cigaban shi yana kungiyar Arsenal. Chelsea ta yiwa Willilian matsakaicin kwantiraki domin ya gama buga wannan kakar a kungiyar su.

Manema labarai na ESPN sun bayyana cewa Arsenal zasu sanar da maganar siyan dan wasan da zarar Chelsea sun kammala buga wasannin su na gasar Champions League.

SOURCE: HUTUDOLE.COM

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN


KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments