LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Borno ta dauki 35% na kashe-kashen da aka yi a rabin shekarar bana

Alkaluman da Nigeria Security Tracker da CFR ta fitar ya bayyana cewa mutane sama da 5, 600 su ka mutu a watanni shida na farkon shekarar nan. Kamfanin StatiSense da su ka saba tara alkaluma na kasashen Duniya sun ce an rasa wadannan mutane a Najeriya ne daga farkon Junairu zuwa watan Yuli.

Kamar yadda alkaluman su ka nuna, jihar Borno ta dauki akalla 35% na kason kashe-kashen da aka yi a wannan lokaci. Jihar ta rasa rayukan fiye da mutum 2, 000. Legit.ng ta lura cewa jihohi 12 na farko da aka fi fama da kashe-kashe,

duk sun fito ne daga yankin Arewacin kasar. Jihohin Kudancin Najeriya biyar kacal ne su ka fito a cikin sahun 20 na farko. Jihohin su ne: Delta, Ribas, Edo, Bayelsa da kuma Kuros-Riba inda aka rasa rayuka 215.

A shekarar nan babu jihar da ba a samu kashe-kashe ba. Jihar farko da ta fito a wannan mummunan sahu daga Kudancin Najeriya ita ce Delta a yankin Neja-Delta.

Jihar da ta samu karancin adadi ita ce Kebbi inda mutum daya aka rasa a sanadiyyar kashe-kashe a tsawon watanni shida. Sauran fitattun jihohin da ba a samu kashe-kashe su ne Bauchi, Kwara, Jigawa, Kano da birnin tarayya Abuja. A Kano rayuka biyu kacal aka rasa zuwa yanzu.

Ga yadda jerin ya ke: 

Borno: 2,038

Kaduna: 730

Zamfara: 727

Katsina: 565

Benue: 161

Yobe: 149

Taraba: 135

Niger: 130

Adamawa: 119

Sokoto: 111

Filato: 110

Kogi: 88

Delta: 67

Ribas: 51

Edo: 48

Legass: 43

Oyo: 32

Anambra: 30

Bayelsa: 30

Kuros Riba: 30

Ebonyi: 28

Nassarawa: 27

Ondo: 24

Ogun: 23

Habuja: 20

Imo: 16

Abia: 12

Akwa Ibom: 11

Bauchi: 11

Kwara: 8

Osun: 7

Enugu: 6

Jigawa: 6

Ekiti: 4

Kano: 2

Kebbi: 1

(Alkaluma daga: Nigeria Security Tracker / CFR)


Kafin yanzu kun ji cewa Shugaba Hassan Rouhani zai taimakawa kasar Lebanon da kayan magani bayan abin da ya faru a garin Bierut.


SOURCE: LEGIT.NG

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN


KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments