LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Uwa Ta Kashe 'Ya'yanta Guda Biyu Saboda Rashin Kudin Ciyar Da Su

Wata mata mai kimanin shekaru 28 mai suna Abigail Agbubla Tetteh ta fada komar 'yan sanda a Sabongarin Tema dake kasar Ghana bayan an zarge ta da kashe yaranta guda biyu ta hanyar ba su guba.

Yaran mace da namiji wadanda 'yan biyu ne masu kimanin shekaru biyu, an kashe su ne da maganin bera a daren ranar Larabar makon da ya gabata.

An kulle su ne a daki, inda har sai zuwa wayewar gari da ake neman su sai aka gano cewa mahaifiyar ta su ta kashe su ne daga bisani ta gudu amma aka kamo ta aka mika ta ga jami'an tsaro.

Wata majiya ta rawaito cewa matar tana yawan korafin cewa mijinta ya gudu ya bar ta ba ya kula da ita da yaran, wanda hakan ya sa ta yanke wannan danyen hukunci.

SOURCE: SHAFIN RARIYA NA FACEBOOK

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN


KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments