LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Hatsarin Mota da Babur mai kafa Uku Yayi Sanadin Mutuwar Mutum 2 A jihar Kano

Wani yaro tare da karamar yarinya sun rasa ransu a wani hatsarin mota da ya afku a jihar Kano bayan da wata Tirela tai Awan gaba da baburin A dai-daita Sahu.

Rahotanni daga jihar Kano sun bayyana cewa, Hadarin ya faru ne a Sabon Titin Panshekara da misalin karfe 2:30 na yamma a ranar Talata.

Baburin na dauke da Direba tare da fasinjoji mutum uku da suka hada da wata mata tare da ‘ya’yan ta guda biyu wadanda suka samu mummunan raunuka.

A cewar Direban Baburin Aminu Abdullahi ya bayyana cewa, Motar tai Awan gaba da Baburin nasa ne a dai-dai lokacin da ke kokarin kaucewa motar.

“Kwai Naji An buge mu kafun in an kara sai ji Nai jini na fita daga kafa ta. inji shi

Wani Shaidar Gani da Ido Mai suna Sharif Jikan Nana ya shaida cewa Motar na dauke ne da Fataucin dabbobi.

A cewarsa “Direban Adaidaita Sahu da fasinjojin sun shafe kusan mintoci 40 a karkashin motar kafin a fitar da su.”

Rundunar kiyaye hadurra ta jihar Kano ta tabbatar da mutuwar mutum biyu.


SOURCE: HUTUDOLE.COM

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN


KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments