LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Kalli Vedion Yanda Fusatattun matasa suka farke rufin majalisar Edo, suka sace sandar iko

Wasu fusatattun matasa sun farke rufin ginin majlisar dokokin jihar Edo tare da sace sandar ikon zaman majalisar. Da safiyar yau, Alhamis, ne 'yan sanda suka mamaye farfajiyar majalisar jihar Edo, sa'o'i kadan bayan tsige mataimakin kakakin majalisar, Yekini Idiaye, wanda 'yan majalisar jihar suka yi yayin zaman majalisar a Benin.

Dan majalisar mai wakiltar mazabar Akoko-Edo ta 1 da wasu 'yan majalisa hudu, a ranar Litinin, sun bayyana goyon bayansu ga dan takarar kujerar gwamna a karkashin jam'iyyar APC, Fasto Osagie Ize-Iyamu.

Wadanda suka bi ayarin Idiaye sune Emmanuel Agbaje mai wakiltar mazabar Akoko-Edo ta biyu, Nosayaba Okunbor mai wakiltar mazabar Orhionmwon ta gabas, Dumez Ugiagbe mai wakiltar mazabar Ovia ta arewa maso gabas.


Duk sun bayanna goyon bayansu ga Fasto Ize-Iyamu a gidan sa da ke Benin. Amma kuma Roland Asoro, mai wakiltar mazabar Orhionmwon II an nada shi a matsayin mataimakin kakakin.

Sai dai, a yayin da majalisar ke zamanta wasu gungun matasa sun dira majalisar domin nuna goyon bayansu da biyayya ga gwamna Godwin Obaseki, wanda ke takarar neman tazarce a karkashin inuwar jam'iyyar PDP.

Ana zargin cewa za a yi amfani da mambobin majalisar dokokin jihar Edo da jam'iyyar APC keda rinjaye domin tsige gwamna Obaseki gabanin zaben da INEC za ta gudanar a cikin watan Satumba.

Wannan ba shine karo na farko da matasa su ka fara cire rufin majalisar jihar dokokin jihar Edo ba, hakan ta taba faruwa a shekarar 2014 bayan barkewar rikici a tsakanin mambobin APC da PDP a majalisar

SOURCE: LEGIT.NG

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN


KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments