LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Wata sabuwa: Yahaya Bello ya tona asirin ‘yan siyasar da suke amfani da COVID-19 suna sanya al’umma cikin tashin hankaliA jiya Alhamis ne 2 ga watan Yuli, gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya zargi ‘yan siyasar Najeriya da amfani da annobar COVID-19 a matsayin hanyar wasa da rayukan al’ummar Najeriya.

Haka kuma ya kara da cewa cutar ta COVID-19 ba sabuwar cuta ba ce.

Gwamnan yayi wannan zargi ne a lokacin da yake magana da mambobin kwamitin amintattu na gidauniyar tunawa da Sir Ahmadu Bello, wadanda suka kai masa ziyara, rahoton The Nation.

Bello wanda ya ce ‘yan Najeriya suna cikin mawuyacin hali, ya dora laifin akan dokar hana zirga-zirga da aka yi, inda ya ce an san hakan zai sanya al’umma cikin wahala rayuwa.

Ya ce kamata yayi Najeriya tayi amfani da wannan lokaci na annobar ta samar da ayyukan yi kamar irinsu sarrafa takunkumin fuska da za ake fitar dashi zuwa kasashen da suke da cutar.

“Ya kamata mu dakata da wannan wasan. ‘Yan Najeriya suna cikin wani hali. Maimakon sanya dokar hana zirga-zirgar dake sanya mutane cikin halin kaka nakayi, mai yasa baza mu juya lamarin wajen samar da ayyukan yi ba; mu dinga sarrafa takunkumi na fuska da za a dinga fita dashi zuwa kasashen da suke da cutar? Ya ce.

Gwamnan wanda ya ce cutar ta COVID-19 ba sabuwar cuta ba ce, domin kuwa Najeriya tana da hanyar maganin cutar.

Ya bayyana cewa maimakon sanya mutane su cikin wani hali na tashin hankali, Najeriya ta fito da hanyar da za ta kawo karshen wannan cuta.


 KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN
 LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments