LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Na yi mafarkin zan yi kudi ne idan na yiwa yarinya fyade – Cewar Aliyu Adamu

Wani mutumi mai shekaru 42 da aka kama mai suna Aliyu Adamu, ya bayyana cewa yayi mafarki ne idan ya yiwa yarinya da take tsakanin shekara biyar zuwa goma zai yi kudi.

Ya bayyana haka ne a lokacin da rundunar ‘yan sanda suka kama shi suka kai shi ofishin su dake Lafia babban birnin jihar.

Aliyu ya ce: ‘Ni dan yankin Bukan Ari ne dake karamar hukumar Lafia.

“Nayi mafarki cewa idan na yiwa yarinya dake tsakanin shekara biyar zuwa goma zan yi kudi sosai.

“Haka ne ya sanya nabi umarnin abinda na gani a mafarki,” ya ce.

Kwamishinan ‘yan sadan jihar, Mr. Bola Longe, shine ya gabatar da mutumin tare da wasu mutane 44 da suka aikata laifuka daban-daban da suka hada da fyade, fashi da makami, asiri da sauran su.

Ya ce an kama mutumin da laifin yiwa yarinya ‘yar shekara 8 fyade ne.

Kwamishinan ya ce yanzu haka ana cigaba da bincike akan lamarin a ofishin binciken manyan laifuka na SCID.

Haka kuma ‘yan sandan sun sake kama wani mai suna Zakari Mohammed mai shekaru 22, wanda ya fito daga Kofar Hausa, dake cikin karamar hukumar Keffi, da laifin yiwa yaro dan shekara 10 fyade, sannan ya jefo shi waje ta taga.

Ya ce sun samu nasarar kamo shi ne bayan rahoton da suka samu daga mahaifin yaron, wanda ya kai kara ofishin ‘yan sanda na Keffi.

A cewar shi: “A ranar 26 ga watan Yuni, 2020, wani mai suna Abdullahi Abu daga yankin Kurkyo cikin karamar hukumar Lafia, ya kai kara da misalin karfe 12 na rana cewa a wannan ranar da misalin karfe 11 na rana, wani mai suna Mohammed Idris mai shekaru 27, wanda ya fito daga wannan gari ya yiwa wani yaro dan shekara 10 fyade.

“Mutumin ya ja yaron zuwa wani kango, inda ya ce zai bashi kudin kifin da ya siya daga wajen shi.

‘An kama mai laifin inda kuma ya amsa laifinsa,” ya ce.


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN
 LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments