LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Tabbas an bamu wani kason aikin N-Power mu baiwa mutanen mu>>Dan majalisar tarayyaA baya dai kakakin majalisar Dattijai, Sanata Ahmad Lawal ya karyata cewa an basu wani kaso na daukar aikin N-Power.


Saidai shugaban kwamitin dake kula da bangaren rage radadi Talauci na majalisar Wakilai, Abdullahi Balarabe Salaame ya bayyana cewa an ware musu wani kaso na aikin N-Power.

Yace an baiwa ‘yan Majalisar wani kaso na aikinne saboda yanda a baya suka ga yanda ake kashin dankali wajan samun aikin yanda zaka ga wani bangarene kawai na kasarnan ke amfana da abin.

Yace ba duka guraben aikin aka basu ba, wani kaso ne daga ciki. Ya bayyana hakane a hirar da yayi da BBC. Da aka tambayeshi ko ba zasu yi amfani da wannan dama wajan cimma manufofinsu na siyasa ba?

Sai yace ai shima shugaba Buhari da ya fito da tsarin Manufofin siyasarsane yake cimmawa dashi. Yace sun wa mutane alkawurra lokacin da suke kamfe dan haka wannan abu na daya daga cikin amfanuwar da zasuwa mutanensu.


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN
 LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments