--
Coronavirus: Hukumar tara haraji ta Kano ta dakatar da mutane 308 daga aiki

Coronavirus: Hukumar tara haraji ta Kano ta dakatar da mutane 308 daga aiki

Hukumar tara haraji ta jihar Kano, KIRS, ta dakatar da wasu ma'aikata 308 daga aiki na wani ɗan lokaci sakamakon raguwar samun kudaden haraji da jihar ta yi. Shugaban KIRS, Bala Inuwa, shi ne ya sanar da hakan yayin da yake zantawa da manema labarai cikin birnin Kanon Dabo a ranar Laraba.

Wannan lamari kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito, ya faru ne a sakamakon durkushewar tattalin arziki da annobar korona ta haddasa. Ya kuma bayyana cewa an yi watsi da kamfanonin tuntuba guda 60 masu bawa hukumar shawara wadanda kwangilarsu ta kare tun a shekarar 2018 kuma su ke ci gaba da aiki ba bisa ka'ida ba.

Sai dai ya ce kamfanonin da ke da sha'awar ci gaba da wannan kwangila na iya sake nema da shigar da bukatar hakan. Yana mai cewa, "mun dakatar da yarjejeniyar aikin ma'aikatan wucin gadi guda 308 na wani ɗan lokaci har zuwa lokacin da kudaden shiga da gwamnatin jihar ta ke samu zai karu."

"Hukumar KIRS a halin yanzu tana fama da karancin kudade a yayin da ta samu faduwar kusan kashi 70 cikin 100 na kudaden shiga da ta ke samu a kowane wata."

"Saboda haka a halin yanzu hukumar ba za ta iya ci gaba da daukar nauyin biyan albashin ma'aikatan na wucin gadi ba." Shugaban na KIRS ya kuma yi bayanin cewa, matakin karancin kudaden gudanarwa da hukumar ta ke fuskanta a halin yanzu ya kai intaha.

Ya bayyana cewa, "kudaden shiga da gwamnatin jihar take samu a baya bayan nan duk wata bayan bullar annobar korona ba su wuce naira miliyan 500 ba zuwa naira miliyan 700, sabanin naira biliyan 2 da take samu wata-wata kafin bullar cutar."

A wani rahoto da jaridar Legit.ng ta ruwaito, mun samu cewa gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa, da mai dakinsa sun kamu da cutar korona 'yan kwanaki bayan diyarsu ta kamu. Hakan yana kunshe cikin sakon da gwamnan ya wallafa kan shafinsa na Twitter a ranar Laraba, 1 ga watan Yuli.

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN
 LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Coronavirus: Hukumar tara haraji ta Kano ta dakatar da mutane 308 daga aiki "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?