LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

'Ya'yan El-Rufai sun caccaki Atiku bayan dan sa ya yi wa El-Rufai habaiciROHOTON: LEGIT.NG

'Ya'yan Gwamna Nasir El-Rufai, Bashir da Bello, sun caccaki tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, bayan daya daga cikin 'ya'yansa ya yi wa mahaifinsu habaici. Dan Atiku Abubakar mai suna Mustapha, ya yi martani a inda El-Rufai ke shawartar iyaye da su koyar da 'ya'yansu girmama mata tun suna kanana.

A cewar gwamnan, hakan ne kadai zai iya dakile annobar fyade da ke tashe a kwanakin nan. Babu kakkautawa Mustapha Atiku ya je yayi tsokaci a kasan wallafar inda yace "Abun mamaki".Babu jimawa kuwa Bashir El-Rufai ya yi martani inda ya kira sunan Atiku tare da cewa "Irin wannan abun mamakin ne ke faruwa a duk lokacin da mahaifinsa ya yi magana a kan rashawa." Ba tare da bata lokacin ba, Bello El-Rufai ya je ya yi nasa martanin mai zafi inda yace, "Bash, zancen ana yinsa ne a kan darajar mata ba luwadi ko rashawa ba.

"Kada ka damu da sabon angon, tsohon abokin naka ya yi tunanin a yanzu yana fadar shugaban kasa inda yake da daman kaiwa ga NNPC kai tsaye."KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN
 LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments