LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Tambaya: Ko Ƙauracewa Facebook Zai Rusa Kamfanin?Kauracewa na da matukar tasiri – tamkar yadda Facebook ya gani.

A karshen karni na 18, masu rajin bijire wa al’amura sun karfafa gwiwar mutanen Birtaniya, inda suka daina ta’ammali da abincin da bayi suka noma.

Kuma ya yi tasiri. Kimanin mutane 300,000 suka daina sayen sukari, al’amarin da ya kara matsin lambar kawar da bauta.

Fafutikar hana kiyayya ta ‘Stop Hate for Profit campaign’ ita ta baya-bayan nan da aka yi amfani da ita wajen bijire wa tsarin siyasa.

Tana ikirarin cewa shafin sadarwar Facebook ba yayin wani katabus don kawar da nuna wariyar launi da kiyaya daga kafar dandalinsa.

Fafutikar ta ja hankalin jerin manyan kamfanoni kan su cire tallace-tallacensu daga shafukan Facebook, tare da sauran kamfanonin sadarwar sada zumunta na intanet.

A jerin wadanda suka aiwatar da kudirin su ne, Ford da Adidas da HP. Sun bi sawun wadanda suka share fage, wadanda suka hada da Coca-Cola da Unilever da Starbucks.

Shafukan labarai sun bayyana cewa Microsoft sun dakatar da tallace-tallace a shafukan Facebook da Instagram a Mayu, saboda nuna damuwa kan rashin tabbaci game da “”Bayanai marasa kyau” – kamar yadda BBC ya tabbatar.

Kuma sauran kafofin sadarwar intanet, wadanda suka hada da Reddit da Twitch, sun kara matsin lamba ta hanyar daukar matakan shawo kan kiyayya a kashin kansu.

Rashin amincewa
Ko kauracewa za ta cutar da Facebook? Takaitacciyar amsar dai ita ce – E – mafi yawan kudin shigar Facebook na samuwa ne daga tallace-tallace.

David Cumming na cibiyar hada-hadar zuba jari ta Aviva Investors, ya bayyana wa BBC a shirin yau cewa, rashin amincewa, tare da rashin kare mutuntaka na iya “rusa harkokin kasuwanci.”

Ranar Juma’a, Hannun jarin Facebook ya fadi da kashi 8 cikin 100, al’amarin da za a iya hasashen ya kassara shugaban Kamfanin facebook Mark Zuckerberg, ta hanyar asarar fam biliyan shida (£6bn)

Dangane da cewa ko lamarin zai iya girmama – wannan barazana da facebook ke fuskanta a halin yanzu na iya jan tsawon lokaci – shi ne ba a tabbatar ba.

Tashin farko dai, wannan dai ba shi ne kauracewar da aka fara yi wa kamfanin shafin sadarwar sada zumuntar intanet ba.

A shekarar 2017, manyan kamfanoni daya bayan daya sun bayana cewa sun daina yin tallace-tallace a kafar YouTube – bayan da aka sanya talla da da hotunan bidiyon nuna wariya da nuna kyarar mu’amalar jinsi guda.

Waccan kauracewar da aka yi an manta da ita a halin yanzu. YouTube ya sauya tsare-tsaren tallace-tallacensa, saboda haka shekaru uku uwar garken YouTube, wato kamfanin Google ke yin hada-hadarsa cikin jin dadi da kyautatuwar al’amura.

Sannan akwai dalilai da za su tabbatar da cewa wannan kauracewar ba za ta cutar da facebook ba tamkar yadda kake zato.

Dumbin masu karancin kashe kudi

Da farko dai, kamfanoni da dama sun jajirce ne wajen kauracewar ta wata guda a Yuli.

Na biyu, kuma ta yiwu mafi muhimmancin al’amari shi ne, mafi yawan kudin shigar Facebook da ake samu daga tallace-tallace suna zuwa ne daga dubban masu kananan harkokin kasuwanci.

CNN ya ruwaito cewa manyan kamfanoni 100 da ke bayar da talla ga Facebook suna samar wa kamfanin kudin da ya kai Dala biliyan hudu da miliyan 200, bisa kimar alkaluman jaddawalin shekarar da ta wuce. ko kimanin kashi 6 cikin 100 na kudin shigar dandalin.


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN
 LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments