LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Ina tilasta mazaje su dinga kallon mu a lokacin da nake yiwa matayensu fyade – Cewar wani dan fashi

A jiya ne wani dan fashi da makami, ya bayyana dalilin da ya sanya yake yiwa matan aure da ‘yan aiki fyade a gaban mazajensu.

A cewar shi, hakan azabtarwa ce saboda hana shi kudi da suka yi, a lokacin da yaje yin fashi.

Maimakon ya roki gafara ko sassauci, saurayin mai suna Adeniyi Ajayi mai shekaru 27, ya roki ‘yan sanda da su kashe shi maimakon kai shi gidan yari.

Ajayi, wanda yake yin fashi da makami shi daya, rundunar ‘yan sandan SARS ta samu nasarar kama shi a wani otel dake Ijora, yankin kamfanin 7-Up dake jihar Legas.

Yanda yake yin fashin shi kuwa shine, zai shiga cikin gidan mutane ya bukaci su bashi hadin kai ko kuma yaran shi da suka kewaye gidansu su kashe su, bayan karya yake yi shi daya yake fashi abin shi.

Bayan rahoton kama shi ya bazu a yankin Sabo, mutane takwas, wadanda yawancin su ma’aikata ne da lauyoyi, suka isa ofishin ‘yan sandan suka bayyana cewa yayi musu fyade a lokacin fashin shi.

A cikinsu akwai wasu mata guda biyu da suke aiki a wani kamfani a yankin na Sabo, wadanda suka bayyana cewa yayi musu fyade a gaban abokanan aikinsu da tsakar ranar 16 ga watan Yuni.

Da ake tambayarsa, ya amsa laifinsa, inda ya ce: “Kwarai kuwa ina yiwa mata fyade wadanda mazajensu suka ki yarda su bani kudi, da kuma wadanda suka yi kokarin wahalar dani a lokacin dana je fashi.

“Ni daya nake yin fashi na, amma ina bayyana cewa ba ni daya nake zuwa ba, saboda na tsorata mutane, su gane cewa ba ni daya bane.

“Hanya daya ce kawai za abi komai ya wuce, shine ‘yan sanda su kashe ni, saboda idan suka kai ni gidan yari, zan fito kuma idan na fito abin sai yafi haka muni, ni kuma na gaji da takurawa ‘yan Najeriya. Zai fi kyau su kashe ni kawai.”

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN
 LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments