LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Hotuna: Matar da tafi kowa tsufa a duniya tayi murnar cika shekara 134

Wata tsohuwa a yankin Uighur wacce aka bayyana an haifeta a shekarar 1886, ta yi murnar cika shekaru 134 a duniya.

Shafin yada labarai na kasar China, ya bayyana cewa matar mai suna Almihan Seyiti, ita ce macen da tafi kowa jimawa a kasar baki daya, duk da dai har yanzu ba a da tabbaci akan ranar haihuwar ta din.

Idan har abinda jami’an gwamnatin kasar China din suka fada gaskiya ne, Ms Seyiti za ta iya zama macen da tafi kowa tsufa a duniya.
Wani bidiyo da aka dauka, ya nuna tsohuwar matar cikin ‘yan uwa da abokanan arziki an zagaye ta ana tayata murnar a Shule wani karamin kauye dake cikin yankin Xinjiang Uyghur, a yankin arewa maso yammacin China.

Tsohuwar ta bayyana cewa ta zauna tsawon karni uku, kuma ta ga yakin duniya da aka yi guda biyu da idonta.

A shekarar 1903, Ms Seyiti ta yi aure a lokacin da take da shekara 17. Jaridar China News ta ruwaito cewa sun dauko rainon yara guda biyu ne ita da mijinta mace da namiji.

Ta cigaba da zama da ‘yarta bayan mijinta ya mutu a shekarar 1976, sannan dan nata ya mutu a lokacin da ya cika shekara 36 a duniya.

Bidiyon da ya bayyana ya nuna tsohuwar sanye da hula ta kwali a kanta a wajen bikin murnar, haka kuma an nuno ta tana wasa da abin kida na gargajiya, inda take magana da mutanen da suka kawo mata wannan ziyara ta biki.

A shekarar 2013, Ms Seyiti ta zama macen da tafi kowa tsufa a kasar China, inda a lokacin da take da shekaru 127.

Tsohuwar wacce take matukar son wasa da wannan abin kida na gargajiya. Ta ce tana cikin koshin lafiya, tana gani rangadadau, sannan kuma tana jin komai da kunnenta, sai dai kuma bata iya tafiya.

Sai dai kuma kafafen sadarwa na kasashen Turai sun musanta yawan shekarun Ms Seyiti, duk kuwa da takardu na kasar China da suke nuni da ranar haihuwarta, inda ya nuna 25 ga watan Yunin shekarar 1886.

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN
 LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments