LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Ikon Allah: Hotunan jaririya da aka haifa babu hannu da kafafuwaWani abin mamaki ya faru a kasar Indiya, yayin da wata baiwar Allah mai shekara 28 ta haifi jaririya wacce bata da kafa da hannaye, a wani kauye da ake kira da Sakla dake Sironj Tehsil a yankin Vidisha, kamar dai yadda rahotanni suka nuna.

A wani bidiyo da yake ta yawo a nuno matar rike da jaririyar, inda aka nuno ta babu hannu da kafafuwa.


Wata likitar yara da take aiki a asibitin Rajiv Gandhi Smriti dake Sironj, mai suna Dr Suresh Aggarwal, ta bayyana cewa jaririyar tana cike da koshin lafiya.

Sai dai likitocin sun bayyana bukatar sake duba lafiyar jaririyar domin sake tabbatar da koshin lafiyarta sannan kuma su tabbatar da kowacce halitta ta jikinta tana aiki.Likitocin sun bayyana wani ciwo mai suna Tetra-Amelia Syndrome a matsayin ciwon da jaririyar take fama da shi, inda suka ce ya samo asali ne a lokacin da ake sauya kwayar halitta ta WNT3, wanda ba kasafai aka fiya samu ba.

Kamar yadda Dr Prabhakar Tiwari da shugabar Bhopal CMHO suka bayyana, dakyar ake samun jariri guda daya da irin wannan cuta a cikin jarirai 100,000.

Shugabar ta ce wannan shine karo na farko da ta fara ganin jaririya mai irin wannan halitta, duk tsawon lokacin da ta dauka tana aiki.

A shekarar 2011 kuwa, wani bincike da Dr Eva Bermejo Sanchez dake kasar Spain yayi ya ce, ana samun irin wannan jariran ne sau daya a cikin jarirai 71,000.

Mahaifiyar yarinyar tana dauke da cikin jaririyar na tsawon wata biyar a lokacin da aka gano cewa hannu da kafafun jaririyar basa girma.

Bayan likitoci sun basu shawara akan su zubar da cikin, matar tare da saurayinta sun ce suna son jaririyarsu a yadda take a haka.

Haka a shekarar 1982, an haifi wani mai suna Nicholas James Vujicic da irin wannan nakasar.

A yanzu haka Nicholas yayi aure har ma ya haifi ‘ya’ya guda hudu, kuma fitaccen marubuci ne, inda kuma ya ziyarci a kalla kasashe 44 a fadin duniya.

A wata hira da aka yi da matarsa mai suna Kanae, ta bayyana cewa ya sha tsangwama a lokacin da suna yara, saboda yayi kokarin kashe kansa a lokacin da yake da shekara 10 a duniya.KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN
 LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments