LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Cutar Coronavirus za ta kara dilmiya talakawa cikin matsanancin talauci - Buhari Karanta daliliROHOTON: LEGIT.NG

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce ana sa ran adadin talakawan Najeriya zai ninku sau uku sakamakon illan da annobar cutar COVID-19 ta yiwa tattalin arzikin kasa. A takardar da aka saki ranar Laraba, mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina, ya ce Buhari ya bayyana hakan ne a sakon faifan bidiyo da ya aike a taron majalisar dinkin duniya.

A shekarar 2019, rahoton cewa cibiyar lissafi ta kasa NBS ta ce a watan Mayu kadai, adadin yan Najeriya dake rayuwa cikin talauci ya kai 82.9 million. Shugaban kasa ya ce a fadin duniya, mutane 700, kimanin kashi 10 na adadin al'ummmar duniya na cikin matsanancin talauci. Buhari yace: "Wadannan mutane kulli yaumin suna fama da rashin ingantaccen abinci, gidajen zama, kiwon lafiya, ilimi da samun ingantaccen ruwan sha.

"A cikin wannan hali, ana sa ran adadin masu fama da bakin talauci zai ninku sau uku saboda dukkan sassan tattalin arziki sun illantu sosai."


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN
 LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments