LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Ango ya rasu bayan shafawa sama da 'yan biki 100 cutar koronaWani biki a kasar India ya zama wurin raba cutar korona bayan da ango ya rasu sakamakon zazzabi mai zafi. Baya ga haka, ya shafa wa sama da 'yan bikin 100 tare da 'yan uwansa cutar korona. Duk da shawarar da ya bai wa iyayensa na dage bikin, sun ki ji tare da ci gaba da shagalinsu.

Kamar yadda jaridar Hindustan Times ta bayyana, angon mai shekara 30 injinuya ne da ya fara zawo da zazzabi mai zafi tun kafin ranar 15 ga watan Yuni, amma 'yan uwansa sun tilasta shi da ya sha magani don su ci gaba da shagalinsu.

Bikin ya samu halartar sama da mutum 360 a Paliganj. Sa'o'i 48 bayan nan, jikin ango ya rude kuma ya rasu a yayin da suke kan hanyar zuwa asibiti, kamar yadda jaridar ta sanar. Tuni aka kai gawarsa ma'adanar gawawwaki ba tare da an yi masa gwajin cutar ba. Bayan rasuwarsa, dukkan 'yan uwansa makusanta sun bayyana da cutar daga ranar 15 zuwa 19 ga watan Yuni.

Domin dakile yaduwar cutar, an samar da sansani inda aka killace dukkan 'yan bikin sannan aka yi ta diban samfur. Daga cikin 'yan biki, mutum 86 sun tabbata dauke da cutar, Amma kuma amarya bata dauke da cutar.

"Duk da bashi da lafiya tun 14 ga watan Yuni kuma ya so a dage bikin, 'yan uwansa sun ki inda suka yi tunanin asarar da za su tafka sakamakon bikin da suka gama shiryawa," wani dan uwansa ya sanar da Hindustan Times. Wani dan uwan angon wanda bai kamu da cutar ba, ya ce babu wanda yayi tsammanin cutar coronavirus ce ta kama angon. "Saboda yankunan kauye duk babu cutar, hankalinmu kwance yake," dan uwan ya sanar.

"A ranar bikin, ya bayyana da zazzabi mai zafi, lamarin da yasa hankali ya tashi. Mun yi ta fatan ba cutar bace," dan uwan yace. "Ya yi dukkan shirye-shiryen bikin bayan ya sha magani," cewar wani dan uwan.


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN
 LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments