LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Daga karshe: FG ta yi magana a kan bude makarantun gaba da sakandareROHOTON: LEGIT.NG


Gwamnatin tarayya tace har yanzu ba a tsara shiri mai kyau ba da zai sa a bude makarantun gaba da sakandare

Mashiryin PTF, Sani Aliyu, ya bada wannan sanarwar yayin da yake cewa ana kokarin ganin an rage yawan masu kamuwa da cutar

Aliyu ya ce bude makarantu saboda masu kammalawa a wannan shekarar ya zama dole saboda gudun asararta dukkanta Gwamnatin tarayya ta disashe tunanin bude manyan makarantun gaba da sakandare nan kusa. Ta jaddada cewa babu shirin wannan ci gaban kwata-kwata.


A yayin jawabi ga manema labarai a ranar Talata, 30 ga watan Yuni, Sani Aliyu ya sanar da hakan a yayin da ake shiga sabon kashi na kulle a kasar nan. Matsayar Aliyu ta zo ne bayan gwamnatin tarayya ta sanar da bude makarantu amma ga masu kammalawa a wannan shekarar a fadin kasar nan.


Aliyu ya ce gwamnatin ba za ta yi hakuri ko wani yunkuri da zai zama zagon kasa ga kokarinta ba ta hanyar bude manyan makarantun gaba da sakandire. Ya kara da cewa dukkan matakan da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aminta da su, ya yi hakan ne saboda a rage yawan masu cutar a kasar nan.

Aliyu ya ce ya zama dole a bude makarantu don masu kammalawa don gujewa asarar wannan shekarar dukkanta saboda annobar Coronavirus.


Ya kara da cewa, gwamnatin tarayya za ta dauka matakai tsaurara wurin tabbatar da cewa sashen ilimin kasar nan bai yi asarar shekarar daya ba cif saboda annobar korona.

"A takaice, babu wani shiri na bude manyan makarantun gaba da sakandare har sai mun ga yawan masu kamuwa da cutar a kullum suna raguwa," Aliyu yace a wani shirin gidan rediyo.

A ranar Litinin da ta gabata, gwamnatin tarayya ta amince da bude makarantu a fadin kasar nan. Hakan ya biyo bayan taron da ya wakana tsakanin kwamitin yaki da cutar korona na fadar shugaban kasa da shugaban kasa Muhammadu Buhari. Kamar yadda gwamnatin tarayyar ta bayyana,

azuzuwan da za su koma bakin karatun sun hada da: 1. Aji shida na dukkan makarantun firamare. 2. Daliban aji uku da na aji shida na makarantun sakandaren da ke fadin kasar nan.


Hakazalika, gwamnatin tarayyar ta amince da bude shige da fice tsakanin jihohin kasar nan, amma matukar ba a zarta lokutan doka baKU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN
 LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments