--
Ina garkuwa da mutane ne domin tara kudin sadaka - Malami

Ina garkuwa da mutane ne domin tara kudin sadaka - Malami



Rundunar 'yan sanda ta gurfanar da malamin coci, Adetokunbo Adenokpo, bisa zarginsa da yin garkuwa mutane - Malamin cocin ya ce ya yanke shawarar shiga harkar garkuwa domin tara kudaden da zai rabawa mabukata sadaka

Rundunar 'yan sanda ta ce malamin cocin ya yiwa dan aiken allurar anesthesia domin galabaitar da shi don basu saukin daure shi Rundunar 'yan sandan Nigeria a ranar Laraba ta gurfanar da wani tsohon malamin coci, Adetokunbo Adenokpo, bisa zarginsa da yin garkuwa da wani dan aike.

Bayan yin garkuwa da dan aikine, Mr Adenokpo ya boye shi a dakin da ke karkashin cocin, a Sagamu, jihar Lagos. Jami'in hulda d jama'a na rundunar DCP Frank Mba, ya gurfanar da Adenokpo tare da wasu mutane 34 da ake zarginsu da laifuka daban daban, a shelkwatar rundunar da ke yaki da fashi da makami a Abuja, a ranar Laraba.

Malamin cocin ya ce ya yanke shawarar shiga harkar garkuwa domin tara kudaden da zai rabawa mabukata sadaka. Ya ce duba da cewa bukukuwan babbar Sallah na gabatowa, ba shi da kudi, dole ya nemi kudin da zai sai kayayyaki kamar shinkafa, wake, rago d.s domin rabawa mabukata. Malamin cocin ya ce shirin bayar da tallafin bai tsaya akan addinin kirista kawai ba, har da sauran addinai.

 DCP Mba ya ce dan aiken Job Ekpe Jonathan, na aiki ne da kamfanin tura sakonni na Glory Master, ya shiga komar Adenokpo da tawagarsa ne a lokacin da ya kai wasu kayayyaki cocin. Mba ya ce malamin cocin, wanda shine shugaban cocin Newlife Church of God da ke Sagamu,

ya yiwa dan aiken allurar anesthesia domin galabaitar da shi don basu saukin daure shi. Rundunar 'yan sanda ta kaddamar da bincike da kuma samun damar ceto Jonathan a inda aka daureshi, wani daki dake karkashin cocin.

Malamin cocin, wanda aka cafkeshi tare abokan aikinsa, ya ce yayi shekaru 22 a harkar malinta, bayan da ya samu horo a Ibadan. "A cocina, muna da shirin bayar da sadaka, inda muke raba kayan abinci da na masarufi ga mabuka, kuma hakan ya bunkasa a lokacin COVID-19.

"Ina jin takaici idan mutane suka zo neman taimako a wajena, alhalin bani da kudi a asusun bankna," a cewarsa. Ya ce an gina dakin karkashin kasar ne inda ya boye Jonathan lokacin da aka kai masa farmaki kwanakin baya, kuma anyi shine domin ya zama mafakarsa idan aka kawo masa hari.

Ya ce yana da wasu matasa da ke bashi kariya. "Makonnin da suka wuce, na fahimci kudina sun kare. Sai na yi tunanin yin wani abu ga Ileya don samun buhunan shinkafa, wake, man ja da sauran kayan da za a rabawa mabukata.

"Sai nayi shawarar mu yiwa kamfanoni masu arziki gadar zare, ta hakan zamu rinka tara kudaden da zamu tallafawa mabukata. "Mu uku ne muka yi garkuwa da Jonathan da nufin tara kudin da zamu rabawa Ileya. Na yi masa allura ne saboda naga yana kokarin guduwa, ba na so kuma aji masa rauni," a cewarsa.


SOURCE: LEGIT.NG

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Ina garkuwa da mutane ne domin tara kudin sadaka - Malami"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?