--
Boko Haram: Ba mu amince da matakin gwamnatin na amsar tubabbun 'yan ƙungiyar ba

Boko Haram: Ba mu amince da matakin gwamnatin na amsar tubabbun 'yan ƙungiyar ba


Wadanda aka kashe wa mazaje ko 'yan uwa a rikicin Boko Haram, sun ce ya kamata gwamnatin Najeriya ta sake tunani a kan batun shigar da tubabbun `yan Boko-Haram cikin al`umma bayan an sauya musu tunani.

Mutanen sun ce mai hali fa da wuya ya sake halinsa, don haka wannan mataki na gwamnati, akwai lauje cikin nadi.

Wata mata da aka 'yan Boko Haram din suka kashe wa miji sannan suka barta da 'ya'ya hudu, ta shaida wa BBC cewa " Abin fa da zafi, an kashe mijina a gabana, an barni da 'ya'ya kanana guda hudu, kasan dai har in mutu ba zan manta da wannan ranar ba".

Ta ce, " Ba tallafi ba, ba komai ba an barka da 'ya'ya hudu, ka duba rayuwar nan da ake ciki wata rana idan an ci wata rana ba za a ci ba, sannan a ce 'yan Boko Haram su tuba a basu kulawa, mu da muka shafe shekara shida muna cikin kangi ba a kula damu ba sai wanda suka fito daga daji wai zai nemi tuba a ce za a kula da shi".

Matar ta ci gaba da cewa, " A gaskiya gwamnati bata yi adalci a kan wannan ba, don ni sai naje na yi wanke-wanke na samu kudi sannan zan ciyar da 'ya'yana".

Shi ma wani da aka kashe wa 'yan uwa na jini har mutum hudu ya ce, " Sun kashe mana 'yan uwa, sun kore mu daga muhallanmu, to yanzu wadannan mutanen su ne zamu zo mu sake zama da su?".

Ya ce, " To yanzu so ake idan muka gansu mu ma mu dau fansa ne?, to za a samu matsala sosai, babu wani tunani da za a sauyawa dan adam fa".

A `yan kwanakin nan ne gwamnatin Najeriyar ta yaye fiye da mayakan Boko Haram 600 da suka tuba, bayan an koya musu sana`o`i don dagaro da kai.

Wasu dai na ganin cewa ba dai-dai ba ne gatan da gwamnatin ta yi wa mayakan Boko Haram din, alhali `ya`ya da dangin mutanen da suka kashe na rayuwa cikin kunci.

A Najeriya, ana ci gaba da sukar shirin gwamnatin kasar na sake shigar da tubabbun `yan Boko-Haram cikin al`umma bayan an sauya musu tunani.

Irin kulawa ko yadda gwamnatin Najeriyar ke tattalin tubabbun mayakan Boko Haram din na cikin abin da ya ja mata suka, musamman yadda aka kebe su a wuri na musamman, ana koya musu sana`o`i, ga kuma bikin da ake yi a yaye su, inda ake dinka musu sutura ta bai daya… sabanin yadda ake takura mutanen da suka ɗai-ɗaita a sansanonin masu gudun-hijira.

Wannan ya sa al`ummomi da shugabannin jama`a da ke shiyyar arewa-maso-gabashin Najeriya, inda rikicn boko haram din ya fi kamari na sukar shirin, suna cewa gwamnati na tuya tana mantawa da albasa, don haka da wuya shirin ya yi nasara.

To sai dai a nasu bangaren, mahukunta a Najeriyar sun ce shirin na taimakawa wajen shigar da tubabbun mayakan Boko Haram din, kasancewar a tsakaninsu akwai wadanda tilasta musu aka yi suka shiga kungiyar...wasu kuma ba su taba zuwa fagen yaki ba ballatana su kashe wani, kuma matukar al`umma ba ta karbe su ba, to karshe sai su koma ruwa.

Koda yake wasu kuma na cewa wannan ba hanzari ba ne, saboda a cewarsu na shiga ban dauka ba, bai fidda barawo.

Amma masana harkokin tsaro na ganin cewa akwai jan aiki a gaban mahukunta na gane masu tuba ta hakika a tsakanin mayakan Boko Haram din.

Sannan, shirin sauya tunanin tubabbun mayakan Boko Haram din ba zai yi tasiri ba sai an saka shugabannin al`umma a ciki don wayar da kan al`umma a kan illar kyamar tsofaffin mayakan, an kuma nuna da gaske ake yi wajen inganta rayuwar wadanda rikicin ya dai-daita.

Source: Bbchausa



KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Boko Haram: Ba mu amince da matakin gwamnatin na amsar tubabbun 'yan ƙungiyar ba"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?