LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Yanzu-yanzu: An sanar da ranar fara jarabawar NECO da NABTEB

Gwamnatin tarayya ta sanar da cewa jarabawar kammala karatun sakandare da hukumar jarabar kasa NECO ke shiryawa zai fara ranar 5 ga Oktoba, 2020 kuma a kammala 18 ga Nuwamba, 2020.

Gwamnatin ta kara da cewa hukumar jarabawar NABTAB za ta kaddamar da nata jarabawan ranar 21 ga Satumba kuma a kammala 15 ga Oktoban, 2020.

Karamin ministan ilimi, Emeka Nwajuiba, ya sanar da ranakun jarabawan ne a karshen tattaunawar kwana biyu da yayi shugabannin hukumomin jarabawar na kasa. A takardar da kakakin ma'aitakar ilimi, Ben Goong, ya saki, ya ce ma'aikatar ta ce za'a a iya fara jarabawa shiga makarantun sakandaren gwamnatin tarayya ranar 17 ga Oktoba, 2020.

Bugu da kari, jarabawar BECE da daliban aji uku a makarantun sakandare da NECO ke shiryawa zai fara ranar 24 ga Agusta kuma a kammala 7 ga Satumba, 2020.
Yanzu-yanzu: An sanar da ranar fara jarabawar NECO da NABTEB Source: Depositphotos


Source: Legit Nigeria KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments