LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Yanzu-yanzu: An sake rufe sakatariyar APC na kasaA karo na biyu a wannan makon, jami'an rundunar 'yan sandan Najeriya sun sake rufe sakatariyar jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa da ke Abuja.

Tun misalin karfe 9 na safiyar yau Alhamis ne wasu manyan motoci kirar hilus da Peugeot 604 suka isa harabar sakatariyar kuma suka zagaye ta.


An umurci ma'aiakatan jam'iyyar da suka iso aiki da wuri su fice daga ofisoshinsu. The Nation ta ruwaito cewa Sufeta Janar na Rundunar Yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu ne ya bayar da umurnin rufe sakatariyar

An umurci Kwamishinan 'yan sanda na birin tarayya Abuja ya tabbata babu wanda ya shiga cikin harabar sakatariyar. Kwamitin gudanar da jam'iyyar, NWC, karkashin jagorancin Hon. Victor Giadom a ranar Talata sun samu amincewar shugaban kasa su kira taron Kwamitin masu zartarwa, NEC, da za a gudanar ta intanet.

Amma 'yan jam'iyyar masu goyon bayan Sanata Abiola Ajimobi sun nuna rashin amincewarsu da kiran taron ta NEC da suka ce ya saba wa dokokin jam'iyyar. Sun ce ba za su hallarci taron ta NEC ba duk da cewa ana sa ran Shugaba Muhammadu Buhari zai hallarci taron daga fadarsa ta Aso Rock ta yanar gizo wata intanet.


Ku kasance da mu don karin bayani ...KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments