--
Siyasar Tinubu Ta Zo Karshe Tunda Aka Yi Masa Gunduwa-gunduwa>>Fani-Kayode

Siyasar Tinubu Ta Zo Karshe Tunda Aka Yi Masa Gunduwa-gunduwa>>Fani-Kayode

Mista Femi Fani-Kayode ya yi kira ga babban jagoran APC Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya yi ritaya daga siyasa, ya kuma janye goyon bayansa ga shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Fani-Kayode ya yi wanan magana ne bayan shugaban kasar ya ayyana Victor Giadom a matsayin mukaddashin shugaban APC a daidai lokacin da kotu ta dakatar da Adams Oshiomhole.

Ga abin da Fani-Kayode ya rubuta: Da farko aka yi fatali da (Adams) Oshiomhole ta kotun daukaka kara. Sai kuma wanda aka so ya maye gurbinsa a jam’iyya, Abiola Ajimobi ya fada gargara.

Femi Fani-Kayode ya kara da cewa:

Sai kuma aka zakulo babban ‘dan adawarsa (Victor) Giadom, wanda Buhari ya yarda da shi a matsayin shugaban jam’iyya na kasa na rikon kwarya.



Abin nufi: Ta karewa Asiwaju Bola Ahmed (Tinubu). An yi jifa da shi daga cikin motar jam’iyyar APC, kuma an yi masa ritaya daga siyasa.



Ana tunanin cewa tsohon gwamnan jihar Legas, Bola Tinubu ya na cikin manyan wadanda su ka tsayawa Adams Oshiomhole, kuma ‘dan siyasar ya na harin kujerar shugaban kasa a 2023.



Masu hasashen siyasa su na ganin cewa wadanda ke adawa da Bola Tinubu ne su ke kokarin yin waje da Adams Oshiomhole daga jam’iyyar APC, wanda hakan na iya kawo masa cikas.

 KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Siyasar Tinubu Ta Zo Karshe Tunda Aka Yi Masa Gunduwa-gunduwa>>Fani-Kayode"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?