--
'Yan sanda ba za su iya kasancewa ko ina ba a koda yaushe - Sufeto Janar

'Yan sanda ba za su iya kasancewa ko ina ba a koda yaushe - Sufeto Janar



A yayin da lamarin tsaro ya ke ci gaba da tabarbarewa a kasar, Sufeto Janar na 'Yan sanda, Muhammadu Adamu, ya ce kada a yi tunanin 'yan sanda za su iya kasancewa ko ina a koda yaushe. A ranar Litinin, 24 ga watan Yuni, babban jami'in dan sandan ya ce 'yan sanda ba za su iya kasancewa ko ina ba a koda yaushe domin bai wa al'umma kariya.

Sufeton na 'yan sanda ya yi furucin hakan ne yayin bikin kaddamar da kwamitin ba da shawara kan harkar tsaro, wanda Sarkin Gombe, Shehu Abubakar da kwamishinan 'yan sandan jihar, Maikudi Shehu suka jagoranta. Adamu wanda mataimakin sufeto janar na 'yan sanda, Halliru Gwandu ya wakilta, ya ce babu wani lokaci mafi dace da ya kamata a kaddamar da wannan kwamiti face yanzu.

A nasa jawaban, Gwamna Inuwa Yahaya na jihar Gombe, ya ce tsaro na da matukar muhimmanci kuma matukar ba a tsaya tsayin-daka wajen inganta shi ba, zaman lafiya ba zai wadata ba.

"Abu mafi fifiko ga kowacce gwamnatin shi ne samar da tsaro, saboda idan aka samu tsaro, za a iya bayar da tabbacin cewa za a kare rayuka kuma za a ci gaba da harkokin kasuwanci," in ji Yahaya. Legit.ng ta ruwaito cewa, a ranar Litinin ne gwamnonin jihohi 19 na Arewa suka gana da shugabannin tsaro na kasa a ofishin mai ba da shawara kan tsaro (NSA), Manjo-Janar Babagana Monguno.

Gwamna Bello Muhammad Matawalle na jihar Zamfara shi ne ya sanar da hakan bayan wata ganawar sirri tare da shugaban ma’aikatan fadar Shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari. A makon jiya ne dai shugaba Muhammadu Buhari ya umarci shugabannin tsaro na kasa da su gana da gwamnnonin Arewa domin bijiro da matakan kawo karshen matsalar tsaro a yankin.

Gwamna Matawalle yayin ganawa da manema labarai na fadar shugaban kasa, ya ce gwamnatinsa tuni ta fara shimfida dabarun magance sha'anin tsaro da ya ki ci ya ki cinyewa a jiharsa. Ya yi bayanin cewa, 'yan ta'addan da suka tuba kuma suka rungumi zaman lafiya an maido su cikin al'umma, yayin da wadanda suka juya baya a kan hakan za su fuskanci fushin hukuma.



KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "'Yan sanda ba za su iya kasancewa ko ina ba a koda yaushe - Sufeto Janar "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?