--
​Rauhani: Amurka Na Neman Tattaunawa Da Iran Ne Saboda Karatowar Zabe

​Rauhani: Amurka Na Neman Tattaunawa Da Iran Ne Saboda Karatowar Zabe



Shugaban kasar Iran Dr. Hassan Rauhani ya bayyana cewa, yunkurin da gwamnatin kasar Amurka take yi a halin yanzu na neman tattaunawa da Iran, yana da alaka ne batun neman kuri’a a zabe mai zuwa.

A yayin zaman majalisar ministocin Iran a yau Laraba a birnin Tehran, shugaba Rauhani ya bayyana cewa, dukkanin yunkurin da mahukuntan Amurka suke ta yi a halin yanzu domin da sunan neman tattaunawa da Iran, magana ce ta siyasa da neman kuri’a.

Ya ce akwai tattaunawar da ake yi tsakanin Iran da Amurka da sauran manyan kasashen duniya a karkashin yarjejeniyar nukiliya da aka cimmawa tare da Iran a 2015, amma Trump ya fitar da Amurka daga wannan yarjejeniya, saboda haka idan Amurka tana bukatar tattaunawa da Iran, to ta dawo cikin yarjejeniyar, kuma ta baiwa Iran da al’ummarta hakuri, kuma ta janye dukkanin takunkuman zalunci da ta kakaba mata.

Rauhani ya ce idan Amurka ta yi haka, to Iran za ta yi aiki da dokokin kasa da kasa, amma karkashin yarjejeniyar da aka cimmawa.



KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "​Rauhani: Amurka Na Neman Tattaunawa Da Iran Ne Saboda Karatowar Zabe"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?