LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Babbar magana: Zan koyawa ‘yata yadda za ta zama fitacciyar karuwa – Mahaifin wata yarinya

Manajan fitaccen mawaki dan kasar Ghana, Shatta Wale, ya bayyana cewa zai koyawa diyar shi yadda za ta zama fitacciyar karuwa, idan har hakane abinda take so a rayuwarta a lokacin da ta cika shekara 18 a duniya.

Manajan wanda ake yiwa lakabi da Bulldog, ya ce ba zai taba tauyewa ‘yarshi hakkinta ba akan kowanne abu da take so idan ta balaga, maimakon haka zai taimaka mata ne wajen ganin ta zama wani abu a rayuwa.

Bulldog yana hira da gidan rediyo na Okay FM ne a ranar Litinin 22 ga watan Yuni, inda yayi wannan maganar.

“Idan ‘yata ta cika shekara 18 kuma ta zo wajena ta ce ‘Baba’ ina so na zama karuwa, ba zan taba kin goyon bayanta ba saboda ta nuna tana so ta zama karuwa” ya bayyanawa dan jaridan da suke magana tare. “Zan dora ta akan hanya ne da za ta zama fitacciyar karuwa.”

Ya ce akwai cigaba da ake samu a karuwanci a yanzu, saboda haka zai taimakawa ‘yar shi wajen ganin ta zama daga cikin fitattu.

“Ba wai na ce Slay Queens karuwai bane, amma na san akwai cigaba da aka samu a harkar karuwanci.

“Akwai karuwai da suke zaune a cikin garinsu, sannan kuma akwai wadanda suke fita kasashen duniya, to zan ce mata ta zama daya daga cikin masu fita kasashen waje.”

“Saboda idan har kana so ka zama daban akan abinda kake yi, dole sai kayi fice a harkar.“

Ya ce akwai karuwai da suke kwanciya da manyan jami’an gwamnati da kuma shugabannin addini, ya ce zai yi kokari wajen ganin ‘yar shi ta kai wannan matsayi. Bulldog dai yana da ‘ya’ya guda uku mata biyu da namiji guda daya.

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments