LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Wanda ake zargi da bata jarirai a Jihar Nasarawa ya shiga hannun Dakarun NSCDCYaro a hannun Dakarun NSCDC Hoto: Daily Trust Source: Twitter 
Jaridar Daily Nigerian ta rahto cewa jami’an hukumar NSCDC sun cafke wani matashi mai shekaru 27 da haihuwa, Ahmadu Yaro, wanda ake zarhi ya yi lalata da jaririya mai watanni uku. Wannan abu ya faru ne a wani kauye da ake kira Adogi, a karamar hukumar Lafia, jihar Nasarawa. A cikin wata guda, an yi wa kananan yara har shida fyade a kauyen Adogi.

Idan ba ku manta ba a ranar 27 ga watan Mayu, aka samu labarin cewa an yi wa wata karamar yarinya mai suna Rukayya Aliyu fyade. Wannan jaririya ba ta wuce kwanaki 90 a Duniya ba. Rahotanni sun bayyana cewa an yi yunkurin yin irin wannan lalata da wata jaririya mai watanni biyu da haihuwa.

An kai wannan hari ne jim kadan bayan an yi lalata da Rukayya Aliyu. An fahimci a kan yi amfani da irin wadannan kananan yara ne wadanda ba su wuce watanni uku zuwa shida da zuwa Duniya ba. Daga nan kuma a jefar da su a kusa da wata makaranta.

Yaro a hannun Dakarun NSCDC Hoto: Daily Trust Source: Twitter 
Ana zargin cewa masu garkuwa da mutane da ‘yan fashi da-dama su na zama a wannan kauye. Haka zalika akwai malaman tsibbu da su ka shahara a jihar da su ke zaune a garin na Adogi. Binciken da jaridar ta yi ya bayyana mata cewa akwai wasu miyagu a kauyen da ke yi wa irin wadannan mutane da su ka saba yin mummunan fyade farautar jarirai da za ayi amfani da su.

Babban jami’in NSCDC na jihar Nasarawa, Gidado Fari, ya ce za a gurfanar da Ahmadu Yaro a gaban kotu. Za a yi wannan ne da zarar an kammala binciken da ake yi a kan matashin. Gidado Fari ya shaidawa ‘yan jarida a ranar Laraba cewa Yaro ya amsa laifinsa, tare da bayyanawa jami’an tsaro yadda ya yi wa wasu kananan yara biyar irin wannan danyen aiki.

Fari ya ce wanda ake zargin ya na ikirarin cewa ya na fama da tabin hankali, abin da ba a iya tabbatarwa ba tukuna. Ana zargin shi kadai ne ya ke addabar mutanen kauyen da fyade.


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments