LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Wata sabuwa: Ya kamata a haramta bayar da sadaki ga mata a lokacin aure – Toni TonesFItacciyar mai amfani da shafukan sadarwa kuma fitacciyar jarumar fina-finan Nollywood, Gbemi Anthonia Adefuye, wacce aka fi sani da Toni Tones, ta ce ya kamata a cire al’adar bayar da sadaki baki daya.

A cewar jarumar, mata ba kadara bane, kuma ba wai anyi su don a siyar bane.

Ta ce: “A haramta al’adar bayar da sadaki. Mata ba kadara bane da ake sayawar.”

Banda jarumar ma dai akwai, fitacciyar mai rajin kare hakkin dan adam, Rene Ahmed, wacce ta taba yin aure sau daya, tun bayan fitowarta ta ce duk wanda zai aureta ba zai biya sadaki ba.

Rene mai shekaru 36 da ta rabu da mijin nata ta ce, idan har ta tashi sake yin aure, ita ce za ta biya kudin sadakin da mijin zai bata.

A cewarta sadaki ba wai dole bane a aure, saboda haka a haramta bayar da shi baki daya.
 KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments