LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Hotuna da bidiyon motocin alfarma da ke garejin Kaftin Ahmed MusaHar a yau, Ahmed Musa na daya daga cikin 'yan kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles masu nasara - Dan wasan kwallon kafar ya yi wasa a Ingila, Netherlands, Rasha kafin ya koma kungiyar Al Nassr ta Saudi Arabia - Dan kwallon kafar da ya saka kwallo sau hudu a raga a yayin gasar kofin duniyar,

ya bayyana garejinsa a yayin da yake buga kwallon tennis Har a yau, Ahmed Musa na daya daga cikin 'yan kwallon kafa masu tarin nasara a Najeriya. Ba a Najeriya kadai ba, za mu iya cewa a duniya saboda irin bajintar da ya gwada a gasar kwallon kafa ta kofin duniya. Dan wasan kungiyar Al Nassr ya jefa kwallo hudu a raga yayin wasan kwallon kafa na kofin duniya. Amma kuma, nasarorinsa ba a wurin kwallon kafa suka tsaya ba inda yake taimakon kungiyarsa a gasa daban-daban.

Tsohon dan kungiyar kwallon kafa ta Leicester City ya bayyana garejinsa ko ma'adanar motocinsa a kafar sada zumuntar zamani a yayin da yake kwallon tennis da wani.
A post shared by Ahmed Musa MON (@ahmedmusa718) on
 A bidiyon da ya wallafa a kafar sada zumuntar zamani ta Instagram, an ga mota kirar Mercedes Benz GWagon wacce kudinta ya ka N120 miliyan tare da Range Rover Velar mai darajar N40 miliyan sai kuma Porsche Macan wacce kudinta zai kai wurin N30 miliyan.
A post shared by Ahmed Musa MON (@ahmedmusa718) on

Ahmad Musa na daga cikin 'yan kungiyar kwallon kafa ta kasar nan da suka yi nasarar samun jinjina a kofin kasashen Afrika da aka yi a kasar Misra. Dan shekaru 27 din ya zama kaftin din kungiyar kwallon kafa ta Najeriya bayan fitar John Obi Mikel daga kungiyar.
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments