LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

​Rasha Ta Sake Caccakar Kasashen Turai Kan Matsayarsu Dangane Da Iran

Gwamnatin kasar Rasha ta mayar da martani mai zafi kan manyan kasashen turai, dangane da matsayar da suka dauka a kan Iran a zaman alkalan hukumar makamashin nukiliya ta duniya IAEA.

Jakadn kasar Rasha a hukumar IAEA Mikhail Ulyanov ya bayyana cewa, kasashen Faransa, Jamus da Burtaniya sun gabatar da kuduri da ke kalubalantar Iran wanda kwamitin alkalan ya amince shi, bayan da wasu daga cikin kasashen da suke mara baya ga kasashen turan suka amince da haka.

Ya ce abin da kasashen turan suka manta da shi, shi ne cewa, ba kashen Rasha da China ne kawai suka yi watsi da wannan kudiri ba, akwai kasashe bakawai wadanda suka yi watsi da shi, wadanda fiye da rabin mutanen duniya suna a cikin wadannan kasashen ne.

Mikhail Ulyanov ya ce, matakin na kasashen turai babu abin da zai jawo illa kara dagula lamurra, wanda hakan ba maslaha ce gare su ba.

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments