LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Sau daya tak nayi ta mutu - Matashin da yayi wa tsohuwa fyade ta mutuWani makiyayi mai shekaru 20 ya yi wa tsohuwa mai shekaru 54 fyade a Ugwulangwu da ke karamar hukumar Ohaozara ta jihar Ebonyi har ta mutu. Laulu Isa dan asalin jihar Nasarawa y shiga hannun 'yan sanda a ranar Talata kuma ya amsa laifinsa.

A yayin zantawa da manema labarai, Isa ya ce sau daya yayi amma sai ta fadi ta mutu, jaridar The Nation ta ruwaito. Ya yi ikirarin cewa illar giya ce ta kwashesa yayi mugun aikin. Ya kara da cewa bashi da burin yi mata fyade amma da ta zage shi bayan taki yarda da shi, sai ya haye mata. Ya ce, "Sunana Laulu Isa daga jihar Nasarawa. Na zo aiki ne Ebonyi.

Na matukar buguwa sai na ga wata mata na tafiya. Na nufeta tare da mika bukatar lalata da ita. "Daga nan ta fara zagina, lamarin da ya fusata ni na rama. A take na fara dukanta. Na kaita kasa na hayeta. Sau daya nayi amma ta fadi ta mutu. "Hankalina ya tashi. Ina bakin ciki, ban taba yin fyade ba. Gara in mutu. Ku yafe min."

Kwamishinan 'yan sandan jihar, Awotunde Awosola ya sanar da manema labarai cewa za a gurfanar da wanda ake zargin. "A ranar 28 ga watan Disamban 2019, wurin karfe 8 na dare aka kama Laolo Isa mai shekaru 20 a kan zarginsa da ake yi da yi wa Mary Okereke mai shekaru 54 fyade har ta mutu," kwamishinan yace.

A wani labarin , wata dalibar jami'ar tarayya da ke Oye Ekiti a jihar Ekiti mai suna Faderera Oloyede ta rasu a dakin saurayinta mai suna Ayo Maliki. Budurwar ta rasu a ranar Talata, 16 ga watan Yunin 2020. Faderera daliba ce da ke aji uku inda take karantar lissafi. Ta ziyarci saurayinta da ke yankin Koko na Iree a jihar Osun tare da wata kawarta mai suna Kemisola Adewusi. Kemisola Adewusi daliba ce a jami'ar Obafemi Awolowo da ke Ile-Ife,

shafin Linda Ikeji ya ruwaito. Kamar yadda wata majiya ta sanar, Maliki ya dafa wa bakinsa shinkafa amma yayin da Oloyede ke ci sai ta fara korafin ciwon ciki. Babu dadewa ta fara amai. A take kuwa ta ce ga garinku duk da yunkurin ceto rayuwarta da Maliki tare da sauran suka yi.


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments