--
Gwamnatin Kano ta haramta goyo a babur, ta bayyana dalili

Gwamnatin Kano ta haramta goyo a babur, ta bayyana dalili



Gwamnatin jihar Kano ta sanar da daukan matakin haramta goyo a kan babur mai kafa biyu a ilahirin fadin jihar. Baffa Babba Dan Agundi, shugaban hukumar kula da zirga - zirgar ababen hawa a Kano (KAROTA), ya kare gwamnatin jihar Kano a kan daukan wannan mataki. Yayin hirarsa da BBC, Baffa ya ce gwamnati ta dauki matakin ne saboda wasu mutane na kokarin dawo da sana'ar acaba a jihar.

A cewarsa, dokar, ta hana goyo a babur, za ta faera aiki ne daga ranar Alhamis, 18 ga watan Yuni. Da ya ke mayar da martani ga masu amfani da babura domin saukakawa kansu sufuri, Baffa ya ce gwamnati ba ta dauki matakin domin muzgunawa jama'a ba, sai don magance matsalar da ake fuskanta ta shigowa da mutane cikin Kano ta barauniyar hanya

Ma su amfani da babura a jihar sun nuna rashin jin dadinsu a kan matakin da gwamnati ta dauka. A cewar Baffa, gwamnati ta dauki matakin ne domin karfafa dokar tarayya ta hana bulaguro zuwa jihohi saboda dakile yaduwar annobar korona.

Gwamnatin Kano, lokacin mulkin tsohon gwamna, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, ta fara haramta sana'ar acaba a shekarar 2013. Ta dauki matakin ne yayin da hare - haren mayakan kungiyar Boko Haram suka yawaita a jihar a wancan lokacin.



KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Gwamnatin Kano ta haramta goyo a babur, ta bayyana dalili "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?