LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Ban taba nadamar abinda nayi wa Ministan Buhari ba - Dan jaridaRotimi Jolayemi, dan jaridar da aka tsare sakamakon cin mutuncin ministan yada labarai da al'adu, Lai Mohammed, ya sanar da jaridar Premium Times cewa baya nadamar abinda ya aikata. Jolayemi, wanda shine jagoran wani shiri mai suna 'Bi aye se ri' da gidan rediyon jihar Osun ke shiryawa, ya shiga hannun 'yan sanda a ranar 5 ga watan Mayu.

Amma kuma, a ranar Juma'a, hukumar 'yan sandan Najeriya ta sakesa bayan amincewar babban kotun tarayya da ke Abuja da bada belinsa. Kafin ranar Juma'a, masu rajin kare hakkin dan Adam da kungiyoyi masu zaman kansu na ta kira ga gwamnati da ta sako shi tare da zargin minista Lai Mohammed da amfani da karfin ikonsa ba ta yadda ya dace ba.

Duk da an sakesa, an gano cewa Jolayemi na wani otal a Abuja yayin da yake jiran ya saka hannu a wasu takardu a ranar Juma'a kafin ya koma jihar Kwara. A yayin zantawa da Premium Times a safiyar Litinin, ya tabbatar da cewa an damke matarsa Dorcas Jolayemi na kwanaki takwas duk a kokarinsu na kama shi.

Hakazalika, ya tabbatar da cewa an tsare 'yan uwansa Joseph Jolayemi da John Jolayemi na tsawon kwanaki biyu. A yayin tsokaci a kan abinda ya faru da shi a Abuja, ya ce "'Yan sandan da suka tsareni sun karbeni hannu bibbiyu ba tare da hantara ba. Sun san aikinsu." "Bayan an daukeni daga Ilorin zuwa Abuja, 'yan sandan sun kula da ni sosai.

Komai a karamce suke min. A lokacin da muka isa Abuja, AIG ya bukacesu da su kula da mu. Ba a azabtar dani ba. Komai cike da kwarewa suke yi," yace. A lokacin da aka tambayeshi ko yayi nadamar wakar da ya fitar wacce ta sa aka tsaresa, ya ce, "Bana nadama ko kadan kuma ba zan taba nadama ba." "Ina nan a matsayata ba zan sauya ba," Jolayemi ya kara da cewa.KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments