--
​Najeriya: CBN Ya Ware Naira Bilyan 432 Domin Tallafa Wa Manoma

​Najeriya: CBN Ya Ware Naira Bilyan 432 Domin Tallafa Wa Manoma



Babban Bankin Tarayyar Najeriya CBN ya bayyana cewa ya ware zunzurutun kudi Naira bilyan 432 domin tallafa wa da kuma inganta noman wasu kayayyakin gona a daminar 2020.

Jaridar Premium Times ta bayar da rahoton cewa, bangarorin da za a ware wa kudin sun hada da noman shinkafa, kiwon dabbobi, noman rogo, masara, auduga, man ja, kiwon kaji da kuma noman kifi.

CBN ya ce wannan shiri ne aka yi domin inganta tsarin ayyukan noma a kasar, ta yadda abinci ba zai yanke a Najeriya a wannan shekara ba.

Hukumar kididdiga ta kasa (NBS) ta sanar da cewa tsadar rayuwa a watan Mayu ta tsananta fiye da shekaru biyu da suka gabata.

NBS ta ce tsadar rayuwa ta karu ne da kashi 12.4 a cikin watan Mayu da ya gabata, wanda kuma a cewar hukumar, tashin gwauron zabin da kayan masarufi suka ne ya haddasa wannan kuncin rayuwa, wanda kuma batun bullar cutar corona ne ya kara ruruta wannan matsala.


 KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "​Najeriya: CBN Ya Ware Naira Bilyan 432 Domin Tallafa Wa Manoma"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?