LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

An rusa ginin ofishin jakadancin Najeriya da ke GhanaMinistan harkokin wajen Najeriya, Geoffrey Onyeama, ya yi tir da hare-hare biyu da wasu mutane da ba a san ko su wa ye ba suka kai a ofishin jakadancin kasar da ke Accra, babban birnin Ghana.

Ministan ya bayyana haka ne a sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Lahadi.

"Muna yin tir da hare-hare biyu da masu aikata laifi da ba a san ko su wane ne ba suka kai a wani gida da ke ofishin jakadancinmu a Accra, Ghana inda aka yi amfani da babbar motar rusa gini wajen rusa gidan," in ji Mr Onyeama.

Ya kara da cewa gwamnatin Najeriya tana tattaunawa da takwararta ta Ghana kan batun kuma ta bukaci a dauki matakin gaggawa domin gano mutanen da suka yi wannan aika-aika.

Ya bukaci a bayar da cikakken tsaro ga 'yan Najeriya da kadarorinsu da ke Ghana.

 KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657


Post a comment

0 Comments